Tsohon Ministan Noma da Albarkatun Ruwa zamanin marigayi Shugaban Kasa Umaru Musa ’Yar’aduwa, Dokta Abba Sayyadi Ruma, ya rasu.
Ya rasu yana da shekara 59, kuma ya bar mata biyu da ’ya’ya tara.
- Hizba ta kama matashin da ke kokarin sayar da kansa a Kano
- Magidanci ya yi wa kanwar matarsa mai shekara 5 fyade
Aminiya ta gano cewa tsohon Ministan ya riga mu gidan gaskiya ne a wani asibiti da ke birnin Landan na kasar Birtaniya.
Da yake tabbatar da rasuwar, kawu a wajensa, kuma Danwairen Katsina, Alhaji Sada Salisu Ruma, ya ce Dokta Abba ya yi fama da larurar ciwon suga ne kafin ya rasu da safiyar ranar Laraba.
An dai haifi marigayin ne a shekarar 1962, kuma ana ganinsa a matsayin daya daga cikin wadanda suka fi karfin fada a ji a zamanin gwamnatin marigayi ’Yar’aduwa.