Tsohon Ministan Sadarwa na kasar Afghanistan, Sayed Sadaat, ya koma dan aike a wani gidan sayar da abinci a kasar Jamus.
Yanzu tsohon minista Sadaat na yawo ne a kan keke domin kai wa kwastomomin gidan abincin da yake aiki abinci a inda suke bukata.
Sadaat ya bar kasarsa zuwa Jamus ne a watan Satumban 2020 bayan ya shekara biyu a matsayin minista a karkashin Gwamnatin Shugaba Ashraf Ghani.
A ranar 15 ga watan Agustan 2021 ne Shugaba Ashraf Ghani ya tsere daga Afghanistan bayan Taliban ta kwace mulki, ya je birnin Tashkent na kasar Uzbekistan.
Daga baya ya koma birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), wadda ta ba shi mafakar siyasa.
Sadaat ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa wasu mutane na sukar sa kan sabon aikin nasa na dakon abinci a birnin Leipzig na kasar Jamus, amma shi yana ganin “duk aiki aiki ne, ni ban ga wa wani abu na jin kunya ba.
“Ni ban ga wani abu ba! Kujerar minista da na rike a baya aikin jama’a, shi ma wannan aikin na dakon sakon abinci da nake yi a kamfanin Lieferando aikin jama’a ne.
“Ina fatar ganin ’yan siyasa sun yi koyi da hakan, su rika fitowa suna aiki a cikin jama’a ba su je su boye ba,” inji Sadaat.
Tsohon ministan wanda ke da digiri iri-iri a fannonin sadarwar zamani da dangoginsu, ya yi ta fadi-tashin neman aiki a fannin a kasar Jamus, amma hakan bai yiwu ba.
“Ina alfahari da abin da nake yi, in ba haka ba watakila da na zama daga cikin bata-garin ministoci in tara miliyoyin daloli, in sayi katafarun gine-gine da otal-otal a nan Jamus ko a Dubai ba sai na yi wa wani aiki ba.
“Hankalina kwance ina kuma alfahari, ba na jin kunyar komai — shi ya sa nake yin aikin da mai karamin karfi ke yi, ina kuma fata sauran ’yan siyasa za su yi koyi, su fito su ma su rika aiki a cikin jama’a ba su je su yi ta buya ba,” kamar yadda ya shaida wa Reuters.
Da farko tsohon ministan, wanda ke da takardar shaidar zama dan kasar Birtaniya, “Kullum yana halartar ajin koyon harshen Jamusanci, kafin a baya-bayan nan ya samu aikin awa shida na dakon abinci a kamfanin na Lieferando,” inji Reuters.