✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Minista Mahmud Tukur ya rasu

Tsohon Ministan Kasuwanci da Masana'atu, Mahmdu Tukur ya rasu a safiyar Juma'a.

Allah Ya yi wa tsohon Ministan Ciniki da Masana’atu, Dokta Mahmdu Tukur rasuwa a safiyar Juma’a 9 ga Afrilu, 2021.

Dokta Mahmud Tukur, shi ne Shugaban Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) na farko, kuma makusanci ne ga Shugaba Muhammadu Buhari.

Iyalansa sun tabbatar wa Aminiya cewa ya rasu ne a Abuja bayan fama da rashin lafiyar da ta sa aka garzaya da shi zuwa asibiti daga Kaduna a ranar Alhamis da dare.

“Za a kai gawarsa Yola, Jihar Adamawa domin yi masa jana’iza,” inji majiyar tamu.

A lokacin rayuwarsa, Dokta Mahmud Tukur ya taba za darakta a kamfanin Cadbury Nigeria.