Tsohon Minista a zamanin mulkin tsohon Shugaban Kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, Injiniya Bunu Sheriff ya rasu.
Ya rasu ne ranar Lahadi yana da shekara 74 a duniya.
- Najeriya A Yau: Yawan Al’ummar Najeriya: Rahama Ga Kasa Ko Taron Yuyuyu?
- Gambiya: Shugaba Adama Barrow ya sake lashe zabe
Marigayin dai ya taba aiki a ma’aikatu daban-daban, ciki har da ta Tama da Karafa da Wutar Lantarki.
Bugu da kari, Injiniya Sheriff ya taba zama jakadan Najeriya a kasar Faransa.
Da yake tabbatar da rasuwar, Sakataren Zauren Dattawan Borno, Dokta Bulama Mali Gubio, ya bayyana kaduwarsa daga rasuwar.
“Mun kadu matuka da rashinsa, mutumin kirki ne, ko kwana biyu da suka wuce muna tare da shi a Fadar Shehun Borno, babu wanda ya san lokacin mutuwarsa ya kusa. Innalillahi Wa’Inna Ilaihi Raji’un.
“Rasuwarsa na zuwa ne jim kadan bayan ta wani dattijon, Alhaji Tijjani Bolori. Wannan babban rashi ne ga Jihar Borno da ma Najeriya baki daya. Allah Ya sa Aljanna ce makomarsu,” inji Dokta Bulama.