Walter Mondale, tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka ya mutu yana da shekara 93 a duniya.
Wata sanarwa da iyalansa suka fitar a ranar Litinin, ta tabbatar da mutuwarsa sai dai ba su bayyana musabbabin da ya yi ajalinsa ba.
- An harbe Shugaban Chadi, Idriss Deby
- Mazauna sun fusata bayan dakatar da Hakimi kan zargin rungumar baki a Abuja
Mataimakiyar Shugaban Kasar Amurka ta yanzu, Kamala Harris ta bayyana Mondale a matsayin “Mutum nagari wanda ya bar abin koyi ga rayuwar ’yan baya,” kamar yadda ta wallafa a shafinta na twitter.
Shi ma tsohon Shugaban Kasar Amurka, Jimmy Carter, wanda Mondale ya yi masa mataimaki, ya bayyana kaduwarsa kan mutuwar mataimakin nasa.
“Yau ina cikin alhinin mutuwar abokina, Walter Mondale, wanda nake tunanin shi ne kwararren matainmakin shugaban kasa da kasarmu ta taba yi.
“Ina fatan zai huta, ina jajantawa iyalansa da ya bari,” a cewar Carter.
Kafin mutuwarsa, Mondale ya yi mataimakin shugaban kasa a lokacin Shugaba Jimmy Carter daga shekarar 1977 zuwa 1981.
Kazalika, ya zama jakadan Amurka a kasar Japan daga 1993 zuwa 1996.