Tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Obadiah Mailafia, ya riga mu gidan gaskiya.
Wani dan uwansa ya tabbatar wa wakilinmu cewa Mailafia ya rasu a Asibitin Kwararru na Gwagwalada, Abuja, bayan rashin lafiya.
- Jama’ar gari sun kashe ’yan bindiga 13 sun kona su a Sakkwato
- Ana shirin tura Abba Kyari Amurka kan Badakalar Hushpuppi
Ya bayyana cewa kafin rasuwar mamacin, ya shaida masa cewa yana fama da zazzabin cizon sauro da mura.
Ya shaida mana cewa da farko ya kira lambar Mailafia domin ya yi masa godiya kan alherin da ya yi masa, amma ba ta shiga.
Daga baya sai ya kira daya wayar inda marigayin ya shaida masa cewa ya kashe dayar ce saboda ana damun sa a kanta alhali yana bukatar hutu saboda rashin lafiya da yake fama da ita.
Ya ce bayan wayar da suka yi har ya yi masa addu’ar samun sauki, ranar Lahadi da safe kuma sai aka kira shi ana sanar da shi rasuwar Mailafia.
A cewarsa, kungiyar ci gaba al’ummar kauyensu na daga cikin wadanda suka aika musu da sakon ta’aziyya.
A baya-bayan nan dai marigayi Mailafia ya shiga labarai kan tataburzar da ke tsakaninsa da hukumar tsaro ta DSS kan zargin ta’addanci da ya yi wa gwamnoni.