✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohon Mataimakin Babban Sufeton ’Yan Sanda Tambari Yabo ya rasu

Mai Duka ya karbi rayuwar tsohon Mataimakin Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya, AIG Tambari Yabo Muhammad. Tambari Yabo ya rasu a ranar Asabar a birnin…

Mai Duka ya karbi rayuwar tsohon Mataimakin Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya, AIG Tambari Yabo Muhammad.

Tambari Yabo ya rasu a ranar Asabar a birnin Sakkwato da ke Arewa maso Yammacin kasar bayan ya yi fama da ’yar gajeruwar rashin lafiya.

Mai yankan kauna ta yi tsohon kwamishinan ’yan sandan lullubi a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usman Danfodiyo da ke birnin na Shehu.

An gudanar da jana’izarsa da misalin karfe 2.30 na rana a garin Yabo na Karamar Hukumar Yabo ta Jihar.

Gabanin ya kai mukamin Mataimakin Babban Sufeton ’Yan Sanda wato AIG, ya rike mukamin Kwamishinan ’Yan Sanda a Kaduna, Kano da Jihar Legas har sau biyu da kuma Oyo da Zamfara da Imo.