Mai Duka ya karbi rayuwar tsohon Mataimakin Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya, AIG Tambari Yabo Muhammad.
Tambari Yabo ya rasu a ranar Asabar a birnin Sakkwato da ke Arewa maso Yammacin kasar bayan ya yi fama da ’yar gajeruwar rashin lafiya.
- Mai cikin ’yan biyu ta dauki cikin da na uku kafin ta haihu
- ‘Masu leken asiri ne dalilin ci gaban ayyukan ’yan bindiga’
Mai yankan kauna ta yi tsohon kwamishinan ’yan sandan lullubi a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usman Danfodiyo da ke birnin na Shehu.
An gudanar da jana’izarsa da misalin karfe 2.30 na rana a garin Yabo na Karamar Hukumar Yabo ta Jihar.
Gabanin ya kai mukamin Mataimakin Babban Sufeton ’Yan Sanda wato AIG, ya rike mukamin Kwamishinan ’Yan Sanda a Kaduna, Kano da Jihar Legas har sau biyu da kuma Oyo da Zamfara da Imo.