✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohon ma’aikacin Muryar Amurka Ibrahim Ayawa ya rasu

Marigayi Ladan Ayawa tsohon wakilin Aminiya ne a birnin Washington, DC na kasar Amurka

Allah Ya yi wa tsohon ma’aikacin Muryar Amurka, Ibrahim Ladan Ayawa rasuwa.

Marigayi Ladan Ayawa tsohon wakilin Aminiya ne a birnin Washington, DC na kasar Amurka, inda yake turo manyan labarai da hira da manyan ‘yan Najeriya da suka kai ziyara kasar.

Marigayin ya rasu ne bayan gajeriyar jinya da ya yi a asibitin George Washington da ke birnin Washington, DC, kamar yadda Muryar Amurka ta ruwaito.

Ladan Ayawa dan asalin Jihar Neja ne a Najeriya, kuma ya taba zama wakilin Muryar Amurka a Jihar Legas na tsawon lokaci kafin daga bisani ya koma Amurka da aiki.

%d bloggers like this: