Tsohon Kwamishinan Raya Karkara da Cigaban Al’umma na Jihar Kano, Abbas Sani Abbas, ya sauya sheƙa daga Jam’iyyar NNPP zuwa APC.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne, ya sauke Abbas daga muƙaminsa a yayin sauye-sauyen da ya yi a majalisar zartarwar jihar a watan da ya gabata.
- Amurka za ta dawo wa Najeriya N80bn da ta ƙwato daga Diezani
- Yadda gobarar dare ta kashe uwa da ɗanta a Abuja
Hakan ya shafi Sakataren Gwamnati na Jihar da Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati, da wasu kwamishinoni huɗu.
A lokacin wata ziyarar da ya kai wa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin a Kano, ne Abbas ya sanarda ficewarsa daga NNPP zuwa APC a hukumance.
Sanata Barau, ya bayyana wannan labari a shafinsa na sada zumunta a daren Juma’a.
Ya rubuta, “Tare da Shugaban jam’iyyarmu na Jihar Kano, Abdullahi Abbas (Ɗan Sarki, Jikan Sarki), da sauran shugabannin jam’iyya, mun karɓi Hon. Abbas, zuwa jam’iyyarmu.”
Ya ƙara da cewa, “Na tabbatar masa da cikakken goyon bayanmu yayin da muke haɗa kai don gina kyakkyawar makoma ga al’ummar Jihar Kano da ma Najeriya baki ɗaya.”
Sanata Barau, ya kuma yi alƙawarin ci gaba da inganta shugabanci nagari, haɗin kai, da yi wa al’umma hidima.