Tsohon Gwamnan Jihar Borno, Ali Modu Sheriff, ya bayyana kudurinsa na shiga takarar shugabancin jam’iyyar APC mai mulki.
Sheriff wanda ya taba rike shugabancin jam’iyyar PDP, ya bayyana kudurin nasa ne a ranar Laraba a garin Abakiliki na jihar Ebonyi, a yayin ziyarar nuna goyon bayansa ga gwamnan Jihar, David Umahi.
- Rashin aikin yi ka iya ruguza Najeriya —Ministan Kwadago
- Jirgin yaki ya yi wa fararen hula aman wuta a Yobe
A ziyarar da tsohon gwamnan ya kai, wadda ba ta wuce ta minti 20 ba, ya samu tarba daga manyan jami’an gwamnatin jihar.
Sai dai Sheriff da Gwamna Umahi sun kebe inda suka shafe wasu mintuna suna tattaunawa ba tare da an san abin da suka tattauna ba.
“Muna son sanar da kowa cewa uwar jam’iyya ta fitar da lokacin da za a yi takarar shugabancin jam’iyya, don haka zan fito takarar shugabancin,” kamar yadda ya bayyana.
Da yake yaba wa Gwamna Umahi kan kokarin da yake na ciyar da jihar Ebonyi gaba, Sheriff ya shawarce shi da ya zabi wanda ya dace ya gaje shi bayan ya bar mulki.
Da yake nasa jawabin, Gwamna Umahi ya ce kudi na taka muhimmiyar rawa wajen kawo siyasa marar ma’ana, amma yana da tabbacin cewa Sheriff ya dace da shugabancin jam’iyyar APC.