✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Gwamnan Oyo, Alao-Akala, ya rasu

Ya rasu yana da shekara 72.

Tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Christopher Alao-Akala, ya rasu.

Har yanzu dai babu cikakkun bayanai a kan rasuwar tasa, amma wata majiya da ke da kusanci da dan siyasar ta ce ta tabbatar wa Aminiya rasuwar ranar Talata.

Ya rasu yana da shekara 72 a duniya.

An haifi marigayin ranar uku ga watan Yunin shekara ta 1950 a garin Ogbomosho da ke Jihar.

Ya mulki Jihar ne tsakanin shekarar 2007 zuwa 2011.