Tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Christopher Alao-Akala, ya rasu.
Har yanzu dai babu cikakkun bayanai a kan rasuwar tasa, amma wata majiya da ke da kusanci da dan siyasar ta ce ta tabbatar wa Aminiya rasuwar ranar Talata.
- An daure shi shekara 7 saboda ‘rashin saurin intanet’
- NLC ta soki kudurin da ke neman haramta wa ma’aikatan lafiya shiga yajin aiki
Ya rasu yana da shekara 72 a duniya.
An haifi marigayin ranar uku ga watan Yunin shekara ta 1950 a garin Ogbomosho da ke Jihar.
Ya mulki Jihar ne tsakanin shekarar 2007 zuwa 2011.