Tsohon dan wasan gaban kungiyar Super Eagles ta Najeriya, Barnabas Imenger, ya rasu.
Barnabas Imenger, ya rasu ne ranar Lahadi a cikin dare bayan fama da jinya a Babbar Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Makurdi, Jihar Binuwai.
- Matsalar tsaro na barazana ga kasancewar Najeriya kasa daya – Gwamnonin Arewa
- ’Yan taratsi sun umarci kamfanonin mai su fice daga Akwa Ibom
Tun watan Janairu tsohon Manager kungiyar Lobi Stars a Kasar Zakarun Najeriya (NPFL) ya yi ta fama da rashin lafiyar, inda an yi ta sallamar sa amma rashin lafiyar na sake dawowa.
A lokacin rayuwarsa, Imenger ya yi tashe a matsayin dan wasan kungiyoyion kwallon kafa na El-Kanemi Warriors, BBL Hawks, BCC Lions da wasu kungiyoyin a kasashen Masar da Saudiyya.
Shi ne kuma tsohon ’yan wasan Super Eagles da dansa yake buga wa kungiyar ta Super Eagles.
Dansa, Barnabas Nanen Imenger ya buga wa Super Eagles wasan farko ne a 2012 a wasan kawancen da Najeriya ta buga da Angola a Abuja.