Tsohon dan wasan Ajantina, Diego Maradona ya rasu bayan ya yi fama da ciwon zuciya.
Tsohon dan wasan ya rasu ne mako biyu bayan an sallame shi daga asibiti, inda aka yi masa aiki a kwakwalwarsa.
- Shirin shakatawa na shekara 30 zai bunkasa tattalin arziki —Sterling Bank
- Mamadou Tandja: Nijar ta yi baban rashi —Buhari
Maradona yana daya daga cikin gwarazan ’yan kwallon kafa a duniya, wanda ya taimakawa kasarsa Ajantina wajen lashe gasar Kofin Duniya a shekarar 1986.
Ya buga kwallo a kungiyoyin Boca Juniors da Napoli da Barcelona da sauransu.
A kan tuna dan wasan da cogen da ya yi, inda ya yi amfani da hannunsa wajen zura kwallo a ragar Ingila, wanda ya yi sanadiyar fitar da kasar a Gasar Kofin Duniya ta 1986.