✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

El-Kanemi Warriors ta ci Enyimba 1-0 a Maiduguri

Kungiyar ƙwallon kafa ta El-Kanemi Warriors da ke Maiduguri ta doke Enyimba  da ci ɗaya mai ban haushi

Kungiyar ƙwallon kafa ta El-Kanemi Warriors da ke Maiduguri ta doke Enyimba  da ci ɗaya mai ban haushi, a ci gaba da gasar Firimiyar Nijeriya (NPFL).

Ƙungiyar Enyimba ta kwashi kashinta a hannu ne a yayin wani wasa mai ban sha’awa wanda ya dauki hankulan jama’a a filin wasanni na El-Kanemi Warriors da ke  Maiduguri.

Kwallo daya tilo da ɗan wasan El-Kanemi Warriors, Abbas, ya zura a ragar Enyimba, shi ya kai ƙungiyar ga nasarar da ta samu maki uku.

Wasan, wanda aka fafata a mako mako na bakwai na gasar rukuni na ɗaya, ya yi zafi matuka, kuma kungiyoyin biyu sun taka rawar gani.

Duk da damarmakin cin ƙwallon da bangarorin biyu suka samu, ƙwallon da Abbas ya zura a minti na 42 ne ya yi alƙalanci inda El-kanemi ta sha gaban Enyimba.

Mai bai wa Ƙungiyar Enyimba shawara a fasahar wasa, Yemi Daniel Olanrewaju, ya yaba da ingancin wasan El-Kanemi Warriors da kuma yadda alƙalan suka gudanar da aikinsu cikin adalci.

Ya ce duk da cewa, ya ji matuƙar takaici rashin nasarar da kungiyarsa ta yi a wasan, “amma ina  da mai kwarin gwiwa game da hasashenmu na samun nasarar a  sauran wasanninmu.”

Mashawarcin fasahar taka leda  na El-Kanemi Warriors, Munnir Abdul Aziz, ya nuna jin dadinsa bisa nasarar.

Ya jaddada kudirin kungiyar na mamaye wasannin gida tare da yin kira ga magoya bayansu da su ci gaba da kwazo da nuna goyon bayansu a kowane lokaci.

Wasan dai ya nuna yadda kwallon kafa ke kara samun tagomashi a Jihar Borno, inda magoya bayan kungiyar dama suka cika filin wasan.

Yanzu haka dai El-Kanemi Warriors za su karkata ne ga wasan da za su yi da Kwara United a gida, wanda a baya aka dage saboda ambaliyar ruwa a Maiduguri.

Ana sa ran wasan zai kayatar a yayin da kungiyoyin biyu ke fafutukar neman maki a gasar.