Ƙarar wani abin fashewa mai ƙarfi ya girgiza Barikin Sojoji na Giwa da ke Maiduguri a Jihar Borno.
Tashin abin fashewan ya jefa mazauna unguwannin Polo, Fori, GRA da Jami’ar Maiduguri cikin tashin hankali a cikin dare, kafin wayewar garin Alhamis.
Rundunar ’Yan Sandan Najeriya reshen Jihar Borno, a cikin wata sanarwa ta alaƙanta lamarin da gobara a ma’ajiyar makamai, wadda ta yi sanadiyyar tashin abubuwan fashewa a Barikin Sojoji na Giwa.
Sanarwar da kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ta ce, “Da misalin ƙarfe 10:30 na dare ne gobarar ta yi sanadiyyar tashin abubuwan fashewa a Barikin Sojoji na Giwa wanda ya haddasa ƙara mai ƙarfin gaske.”
- AU ta janye takunkumin da ta ƙaƙaba wa Gabon
- Dokta Bashir ya zama shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Nijeriya
Jami’in ya sanar da haka yana mai kira ga mazauna yankunan da ke Maiduguri su kwantar da hankalinsu.
Hukumar Kashe Gobara ta Ƙasa reshen Jihar Borno ta bayyana cewa jami’an kwana-kwana daga rundunar tsaron Najeriya da hukumar suna ci gaba da aikin shawo kan lamarin.
Ta ƙara da cewa, “Akwai yiwuwar samun ƙarin tashin abubuwan fashewa a yankin don haka kada al’umma su firgita.”
Ta ƙara da cewa, “Binciken farko ya nuna akwai yiwuwar yanayin tsananin zafin da ake dana da shi a Maiduguri a halin yanzu na da alaƙa da tsananin tashin abubuwan fashewan.”