✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon dan kwallon Green Eagles ya rasu

Tsohon dan kwallon kulob din Stationery Stores da ke Legas da kuma kungiyar kwallon kafa ta kasa watau Green Eagles Peter Aneike ya rasu. Ya…

Tsohon dan kwallon kulob din Stationery Stores da ke Legas da kuma kungiyar kwallon kafa ta kasa watau Green Eagles Peter Aneike ya rasu. Ya rasu ne a ranar Litinin 20 ga watan nan da muke ciki a gidansa da ke Legas.

Marigayin, dan kimanin shekara 68 ya dade yana jinyar ciwon sanyi (rheumatism) da ya kubura masa kafafu kuma da hakan ta sa ba iya iya tashi kon yin tafiya.
Peter, ya fara buga wasan kwallonsa ne a shekarar 1967 kafin daga bisani a shekarar 1970 ya buga wa kungiyar kwallon kafa ta Green Eagles.
An shaide shi a mnatsayin dan kwallon da ya yi fice kuma yake jefa kwallaye a raga a wancan lokaci da hakan ta sa wasu suke masa lakabi da ‘Eusebio na Afirka’.
Marigayin ya yi wasan kwallo a kungiyar kwallon kafa ta Green Eagles a wancan lokaci ne da ’yan wasa irin su Mesembe Otu da Sokari Dokubo da Godwin Anosike da Teslim Balogun da Titus Okere da Etin Henshaw da kuma Edet Ben.
An haifi Aneike ne a ranar 2 ga watan Maris na 1947. Ya rasu ya bar mata daya da ’ya’ya shida.