✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon dan kwallon Eagles ya zama Daraktan wasanni a kulob din Monaco

Rahotanni sun tabbatar tsohon dan kwallon Najeriya Super Eagles Micheal Emenalo, dan asalin Najeriya ya zama Daraktan wasanni a kulob din Monaco na Faransa. Emenalo…

Rahotanni sun tabbatar tsohon dan kwallon Najeriya Super Eagles Micheal Emenalo, dan asalin Najeriya ya zama Daraktan wasanni a kulob din Monaco na Faransa.

Emenalo wanda ya ajiye mukamin Daraktan wasanni a kulob din Chelsea na Ingila bayan ya shafe kimanin shekara 10 yana rike da matsayin, ya yi murabus a kulob din ne kimanin makwanni uku da suka gabata inda ya nuna zai dan hutu kafin ya san abin da zai yi nan gaba amma abin mamaki sai ga shi ya koma kulob din Monaco na Faransa a matsayin Daraktan wasanni a kasa da makwanni biyu bayan ya ajiye irin wannan mukami a kulob din Chelsea.

Emenalo wanda yana daga cikin ’yan kwallon Super Eagles da suka wakilci Najeriya a gasar cin kofin duniya a shekarar 1994 ya rike mukamin Daraktan wasanni a kulob din Chelsea har na tsawon shekara 10 kafin ya yi ritaya kimanin makwanni uku da suka gabata.

Ya ce ya koma Monaco ne saboda ya lura kulob din yana tashe a halin yanzu hasalima kulob din ne ya lashe gasar rukunin Faransa (Ligue 1) a kakar wasan da ta wuce.

Sai dai a halin yanzu kulob din yana fuskantar matsala bayan ya sayar da zaratan ’yan kwallonsa ciki har da Kylian Mbappe da ya koma kulob din PSG na Faransa.