✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon dan damben boksin Manny Packuiao ya samu digiri

Tsohon dan damben boksin da yanzu haka ya rungumi harkar siyasa inda ya zama shugaban wata karamar hukuma a kasarsa ta Philippiness ya kammala karatun…

Tsohon dan damben boksin da yanzu haka ya rungumi harkar siyasa inda ya zama shugaban wata karamar hukuma a kasarsa ta Philippiness ya kammala karatun digiri a wata jami’a da ke Makati a Philippines a karshen makon jiya.

Tsohon dan damben ne da kansa ya sanar da haka a shafin sadarwarsa inda ya sanya hotunan saukar karatun digiri tare da dansa da matarsa a zagaye da shi don taya shi murna.

Manny Packuiao ya yi tashe a harkar damben Boksin inda ya lashe manyan kambunan damben boksin na duniya.

An shaide shi a matsayin mutumin da ke son taimakon al’ummarsa da hakan ta sa bayan ya bar harkar damben boksin sai ya tsunduma harkar siyasa.  Al’ummarsa sun zabe shi shugaban wata karamar hukuma da hakan ya sa ya koma karatun jami’a don ya karo ilimi.

A karshen makon jiya ne ya gama karatun inda ya nemi al’umma musamman ’yan kasar Philippines su taya shi murnar kammala karatun digiri don ya samu kwarewar da ta dace wajen yin shugabanci.