✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohon Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya, Tafa Balogun, ya rasu

Ya zama shugaban ’yan sandan Najeriya a 2002

Tsohon Sufeta-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Tafa Balogun, ya rasu.

Wasu majiyoyi daga iyalan mamacin ne suka tabbatar da rayuwarsa a ranar Alhamis, ko da yake ba su yi cikakken bayani a kai ba.

Tafa Balogun dai ya zama shugaban ’yan sandan Najeriya ne a watan Maris don 2022.

An haife shi ranar takwas ga watan Agustan 1947, a garin Ila-Orangun na jihar Osun, kuma shi ne Babban Sufeton ’yan sandan Najeriya na 21.

Kafin nan, ya rike manyan mukamai da dama, cikin har da Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda a Jihar Edo, Kwamishinan ’yan sanda na farko a jihar Delta, sannan ya kuma rike mukamin a jihohin Ribas da Abiya.

Yana rike da matsayin Mataimakin Babban Sufeton ’yan sanda (AIG) mai kula da shiyya ta daya da ke Kano ne aka nada shi Babban Sufeton a 2002.

Sunan shi ya yi tambari a duniya ne a shekarar 2005, lokacin da aka gurfanar da shi a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, bisa zargin satar Dalar Amurka miliyan 100 lokacin yana kan kujera daga lalitar rundunar.

Shari’ar tasa dai ta cika da ce-ce-ku-ce, inda a ranar 29 ga watan Yunin 2005 lokacin da ya yanke jiki ya fadi a gaban kotun.

An dai zarge shi ne da tuhume-tuhume guda 56, inda ya amsa aikata takwas daga ciki, sannan aka yanke masa hukuncin daurin wata shida.

Daga bisani an sake shi a ranar tara ga watan Fabrairun 2006, bayan ya kammala wa’adin.