✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsoho ya kashe daliban jami’a 5 bayan ya yi mankas da giya

Daga a cikin wadanda aka kade har da sabbin dalibai wadanda a ranar Litinin suke fara daukar darussa

Wani tsoho da ya yi mankas da giya ya kade daliban jami’a biyar har lahira da motarsa a kasar Slovekia.

Tsohon mai shekara 60, ya yi cikin daliban da motarsa a lokacin da yake cikin maye, nan take dalibai hudu suka ce ga garinku nan.

Ministan Harkokin Cikin Gida na Slovakia, Roman Milukec, ya ce “Daga a cikin wadanda aka kade har da sabbin dalibai wadanda a ranar Litinin suke fara daukar darussa.”

Tuni dai ’yan sanda suka cika hannu da mutumin, suka kuma bayyana cewa “Nan take dalibai hudu suka rasu, kafin daga baay mutum na biyar ya cika.

“Akwai wani dalibin kuma da ke kwance a rai kwakwai, mutu kwakwai a asibiti‚” baya ga wasu dalibai biyar a aka kai asibiti.

Lamarin dai ya faru ne a ranar Lahadi da dare, a yankin Slovak, hedikwatar Bratislava.

Milukec, ya ce wanda ake zargin na iya shan daurin shekara bakwai zuwa 12 idan aka same shi da laifi.

Ya bayyana cewa, “Duk mutumin da ya sha giya sannan yake tuka abin hawa, to wannan mutumin ya riga ya zama makami”.