✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsoho mai shekara 60 ya yi wa ’yar cikinsa fyade

Wata kotun majistare da ke zamanta unguwar Iyaganku a birnin Ibadan na Jihar Oyo ta tsare wani tsoho bisa zargin yi wa ’yar cikinsa fyade.…

Wata kotun majistare da ke zamanta unguwar Iyaganku a birnin Ibadan na Jihar Oyo ta tsare wani tsoho bisa zargin yi wa ’yar cikinsa fyade.

Ana zargin mutumin mai kimanin shekar 60 ya yi wa ’yar tasa fyade ne a cikin dare.

Alkalin kotun, Misis O.A. Akande ta bayar da umarnin tsare shi har zuwa lokacin da ofishin mai shigar da kara na jihar zai mika rahoton bincikensa.

Daga nan ta dage sauraron karar har zuwa 12 ga watan Nuwamba mai zuwa.

’Yar sanda mai shigar da kara Sajent Gbemisola Adedeji ta shaida wa kotun cewa a ranar 31 ga watan Agusta ne da misalin karfe 10 na safe Mista Aboidun zakke wa diyar tasa mai kimanin shekaru 22 ba tare da amincewarta ba.

Gbemisola ta ce laifin ya saba wa Sashe na 357 na kundin dokokin manyan laifuka na jihar Oyo na shekara ta 2000.