✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsoffin ma’aikatan NECO na neman a biya su bashin haƙƙoƙinsu

Gwamnatin Nijeriya ta maida ritaya abin fargaba a wurin ma'aikata saboda tarin ƙalubalen da ke biyo baya

Tsoffin ma’aikatan Hukumar Shirya Jarabawar (NECO), da suka yi ritaya na neman a biya su haƙƙoƙinsu da suke bin bashi.

Shugaban ƙungiyar tsofffin ma’aikatan, Dokta Abdullahi Rotimi Williams ne ya bayyana hakan a bikin ƙaddamar da hedikwatar kungiyar a Minna, babban birnin Neja.

Shugaban ya kuma koka kan yadda gwamnatin Nijeriya ta maida ritaya abin fargaba a wurin ma’aikata saboda tarin ƙalubalen da ke biyo bayan hakan, musamman maƙalewar haƙƙoƙinsu.

“Da yawa tsoron ritaya ake yi yanzu. Don haka wannan ƙungiyar za ta taimaka wajen rage waɗannan matsalolin.

“Babban ƙalubalen da muke fuskanta shi ne na lafiya. Don haka ina roƙon shugaban hukumar da ya tabbatar cewa daga yanzu an kammala shirye-shiryen da suka kamata kafin ma’aikacin NECO ya yi ritaya.”

Ya kuma ce duk da jagororin hukumar na yanzu sun biya wasu daga cikin haƙƙoƙin nasu, ba a kai ga biyan alawus ɗin ƙarin girma ba, da na tafiye-tafiye ba.