Gwamna Umar Mohammed Bago, ya sanya dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 12 a birnin Minna na Jihar Neja.
Wannan dai na zuwa ne sakamakon hare-haren da ya janyo salwantar rayuka da aka samu a bayan nan a babban birnin.
- Hanyoyin da za a magance rikicin Filato — Masana
- HOTUNA: Yadda Pantami ya kai wa Sheikh Jingir ziyarar ta’aziyya
A cewar gwamnan, an haramta zirga-zirgar baburan ’yan acaɓa da masu Keke Napep daga ƙarfe 6 na yamma zuwa 6 na safiyar kowacce rana.
Gwamnan ya bayyana hakan a yayin wani taro na musamman da ya gudana da masu ruwa da tsaki kan sha’anin tsaro da ya ƙunshi sarakunan gargajiya da shugabannin hukumomin tsaro a Fadar Gwamnatin jihar a ranar Talata.
A yayin da dokar ba ta shafi duk wata buƙatar lafiya ta gaggawa, Bago ya ce ba a buƙatar ganin ababen hawa daga lokacin da dokar ta fara aiki da zummar daƙile matsalar tsaro da babban birnin ke fuskanta.
Ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta zuba ido a yayin da miyagu ke ci gaba da kai hare-hare da kashe mutanen da ba su ji ba kuma ba su gani ba.
Ya umarci dukkan dagatai da masu unguwanni da su tabbatar da ɗaukar bayanan duk wasu baƙi da suka shigo yankunansu.
Kazalika, ya yi gargaɗin cewa duk gidan da aka kama yana bai wa miyagu mafaka ko masu fataucin muggan ƙwayoyi za a rushe shi.
A ’yan kwanakin nan dai birnin Minna na fuskantar matsalar tsaro da ta haɗa da dabanci, hare-hare da kisan kai da sauran miyagun ababe masu ɗaga hankalin mazauna.