Duk da tabbacin ci gaba da amfani da tsoffin kudi da Gwamman Jihar Kaduna ya bai wa talakawansa, jama’ar jihar sun yi dafifi a Babban Bankin Najeriya (CBN) a ranar Juma’a domin mika tsoffin kudinsu.
A ranar Alhamis Gwamna Nasir El-Rufai ya bai wa ’yan jihar tabbacin su ci gaba da amfani da tsoffin takardun N500 da N1,000 duk da cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanar cewa sun daina amfani.
- An ceto jaririyar da mahaifiyarta ta jefa a masai a Kano
- Amurka za ta dawo wa Najeriya $954,000 da tsohon Gwamnan Bayelsa ya sace
El-Rufai ya ce za a ci gaba da amfani da tsoffin kudin a jiharsa zuwa lokacin da Kotun Koli za ta yanke hukunci kan shari’ar da ke gabanta na kalubalantar wa’adin daina amfani da tsoffin kudin.
A jawabin da ya yi wa ’yan kasa ranar Alhamis, Shugaba Buhari ya sanar da tsawaita wa’adin amfani da tsohuwar takardar N200 da kwana 60.
Kana Shugaban Kasar ya bukaci a maida tsoffin N500 da N100 zuwa CBN saboda a cewarsa sun daina amfani.
Sai dai duk da umarnin na Shugaba Buhari, Gwamna El-Rufai ya sha alawashi rufe duk wani wuri da aka kama a jiharsa ya ki karbar tsoffin N500 da N1000 a jihar.
Binciken Aminiya ya gano cewa asubanci wasu mazauna jihar suka yi zuwa CBN don mika tsoffin kudin da ke hannunsu gudun kada su tafka asara.
Badamasi Aliyu na daya daga cikin wadanda lamarin ya shsafa, ya shaida mana cewa, “Ni mazaunin Kawo ne cikin Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa. Tun karfe 3 na dare na zo nan na hau layi, ni ne mai lamba 134.
“Dole na kama otel da ke kusa na kwana domin in samu isowa da wuri, lamarin babu sauki amma ina fata zan samu damar mika kudina.”
Haka ita ma Mary Auta, ta ce ta ziyarci bankin ranar Alhsmis ba ta samu biyan bukata ba.
“Na zo nan ranar Alhamis, babu wani jami’in bankin da ya saurare mu. Ina fatan yau (Juma’a) za su saurare mu,” in ji ta.
Da yake maida martani, wani jami’in CBN, Mukhtar Maigamo, ya ce shirin ya kankama kuma ana kula jama’a daya bayan daya.
A cewarsa, “Da yawansu abin da suke dauke da shi bai kai N500, 000 ba, kuma abin da aka ba mu damar karba shi ne daga kan N500,000 zuwa sama,” in ji shi.