Kawo yanzu jihohi 12 ne suka garzaya Kotun Koli suna neman kotun ta soke umarnin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na haramta amfani da tsoffin N500 da N1,000 da kuma tsawaita wa’adin tsohuwar N200.
Jihohin su ne Kaduna, Kano, Jigawa, Kogi, Zamfara, Sakkwato, Legas, Ondo da Ekiti, Katsina, Ogun, da kuna Kuros Riba.
- Canjin kudi: Dalilin Tinubu ke tausaya wa talakawan Najeriya
- Buhari ya gama yi wa PDP kamfe da halin da ya jefa Najeriya – Nafada
Cikin karar da suka shigar ranar Juma’a, baki daya jihohin sun bukaci Kotun Koli ta yi watsasi da umarnin da Buhari ya bai wa Babban Bankin Najeriya (CBN), yayin jawabinsa ga ’yan kasa a ranar Alhamis.
Jihohin sun shaida wa kotun cewa umarnin na Buhari ya saba wa doka da kuma yi wa Kotun Koli karan tsaye kasancewar batun na gabanta.
A ranar 8 ga Fabrairu Kotun ta ba da umarnin ci gaba da amfani da tsoffin takardun N200 da N500 da N1000 zuwa lokacin da za ta saurari shari’ar.
Tawagar lauyoyin jihohin karkashin jagorancin A.J. Owonikoko (SAN), sun ce Kotun ta sake jadadda wannan umarni nata a ranar 15 ga Fabrairu.
A ranar 15 ga Fabrairu, jagoran alkalan Kotun, Mai Shari’a John Inyang Okoro, ya hada jihohi 10 masu adawa da matakin canjin kudin wuri guda, haka ma masu goyon bayan matakin, da suka hada da Bayelsa da Edo wuri guda kuma a matsayin bangare na masu kare kansu.
Ana sa ran Koutun ta sake zama kan wannan batu a ranar Laraba, 22 ga Fabrairu.