Tsofaffin kansiloli sama da 360 ne suka gudanar da taron addu’ar rokon Allah Ya kawo musu dauki game da hakokkinsu da Gwamnatin Jihar Kano ta ki biyan su.
Tsofaffin kansilolin sun ce yawancinsu sun hadiyi zuciya sun mutu saboda kuncin rayuwa, sannan suka roki gwamnatin jihar da ta dubi halin da suke ciki.
- An yi masa daurin rai da rai kan yi wa ’yar makwabcinsa mai shekara 14 fyade
- Yadda uba da dansa suka lakada wa likita duka a asibiti
A yayin suke zanta Wa da gidan rediyon Freedom da ke Kano, daya daga cikinsu ya ce, “Mun zo a kan Gwamnatin Kano ta tausaya mana ta biya mu hakokkinmu wanda idan an biya mu za mu samu saukin rayuwa.
“A taimaka a dube mu, duk wanda ya gan mu ya san muna cikin wani yanayi.
“Mun yi kansila mun hidimta wa al’umma, mun sauka an bar mu a cikin wani yanayi, yau sati na guda rabona da gidana,” in ji wani daga cikinsu.
Muna sane da su —Gwamnati
Amma da muka tuntubi Ma’aikatar Kananan Hukumomi ta Jihar Kano, kwamishinan ma’aikatar, Lami Sani, ya ce suna sane da hakokkin da tsoffin kansilolin ke bi, amma ya ce yawancinsu tun a lokacin gwamnatocin da suka shude suke bin bashin.
Amma ya ce gwamnatin jihar na bi daki-daki wajen biyan su hakkokinsu da suke bi.
Sai dai ya bukace su da su kara hakuri duba da irin tarin aiki da hakkin al’umomi da ke kan gwamnatin jihar.
Sani ya ce gwamnan jihar, ba shi da muradin tafiya ya bar gwamnati mai zuwa da tarin bashi kamar yadda ya gada a wajen gwamnatocin baya.