Tsinin tsingaro
Tsattsagar tsakin tsintar gero
Tsabar maiwa da dauro
Tsautsayin ga na ta tsiro
Tsakuwar jifa a kwararo
Tuni an samu horo
Babu wake balle ai roro
Miyagu sun makaro
Wuyan al’umma za su shakaro
Dan agwagwa yai doro
Siyasa ce da tasgaro
Makirai na ta taro
Ba su da shanu sun shiga sharo
Anai musu kidan bambaro
Haka dai lamurra suka dauro
Kiren karya suka kirkiro
Haurobiyawa a luro
Dan agwagwa babban toro
Tuni ya gangaro
Na-mujiya duk sun zazzaro
Danboto
Mai damin toto
Tuni ta zama fanko
Tana laluben na koko
Masana sun bayar da rahoto
Tsagalgalewar tsageru
Tsunkule-tsunkulen tsikararru
Tsabagen tsigarewar tsoro
Tsagwaron tsarin tsaro
Tsatsubar tsunburburar tsibirin tsuru-tsuru
Dabarbarun dube-duben Dabai
Kwance kullin kwabbai
Motsin mutsuttsuke matsabbai
Makircin maida kasa kuffai
Falle fama-famai a faifai
’Yan adawa
Na shirin dira wawa
Za su sa ai ta kuwwa
Da Baba suke kokowa
Kura za tai amai da yawa
Mutan Haurobiya
Kar a maishemu baya
An san masu wawushe kaya
Bayan sun yi laya
Yau sun dawo da baya
Tsagera
Na ta yi muku hira
Saboda toshewar basira
Yana neman a amsa masa kira
Lallai a kiyayi larura
An fasko dan gwanjo
Rainon Baba-Ojo
Yai karya ga su Hajjo
Zai taka rawar banjo
Ka lura Usainin-Babajo
Wawurar watsa wuri
Wa-ka-ci-ka-tashin wuri
Watangaririya iri-iri
Wasa da hankali kuri
Wulkita na-mujiya wuri-wuri
Zababbakar zabuka
Zarar zantuka
Zakalkalewar zalaka
Zumun zakuwar zuka
Zarin zagaye-zagayen bukka
An ce kaji sai da tsaba
Akai wa al’umma haba-haba
Ku daina yin marhaba
Da masu maishe da ’ya’ya ’yan daba
Ko ma su zam ’ya’yan dabba
Nai ta huduba
Kususan ga ’ya’yan Abba
Kar su yarda da sakiyar lamba
Don tana da tsananin azaba
Mugun aiki duk mu tuba
Mafita ake nema
Kowa sai ya kama
A tarairayi al’umma
Sai mu samu makama
Turba tagari tai ta zama
An dade ana ta fama
Miyagu na ta fankama
Talakawa wasu sun suma
Fatarsu kamar an yi jima
Mu dai kara himma
A inganta lantarki
Samar da hasken kirki
Mu murza na’urar nikan buski
A samu na sa wa a baki
Ko a daina tsaki
Kar a kawo mana tarnaki
Shasshekar shakar hayaki
Bankar buki
Sunkurun shigar rukuki
Mashakon makogwaro mai makaki
Mai-hular saki
Ya ce yai yaki
Na ce kun ji zuki
Baba yai lakaki
Mai-duka yai mana sauki
’Yan miya tai zaki
Sun lashi maski-maski
Sun cika baki da mumuki
Sau tarin shurin masaki
A lura ’yan gari da baki
Ina kuke ’yan birni
Kui managarcin tunani
Kyawawan ta’adun iyaye da kakanni
Mu daina yi wa juna gani-gani
Cutuka ai musu magani
Ai ta batu na hankali
Talaka da mai hali
Ku fahimci karatun kiskali
Da faskaren kowane kauli
Ta haka ake kwance kulli
Tarin dukiya a baitil-mali
Ba a dauka ai fatali
Kudin gina kasa ake tattali
Aiki ne tuli-tuli
Sukuwar ingarma tai kyau da akawali
Ni da mutanen amana
Rani da damina
Ko an yi zafin rana
Fafutikarmu gyara ya wakana
Nunin ayyuka zai sa a bar magana
A nesanci masu manufar cefane
Dukiyar kasa su danne
Na-mujiyarsu su kanne
Kowace harka sun yi kane-kane
Ba su damu ba ko kasa ta kone
’Yan makaranta sun yi aune
An dai san zabuwa na da zane
A daina yi mana kwane-kwane
An fasko wane da wane
Masu shirin sane
Tsagalgalewar tsigarewar tsageru ta ta’azzara a daukacin Haurobiya, domin Haurobiyawa ba su kyaro wadanda suka kusan cefanar da kasar nan ba, har ta kai ga bayan Babun-burin-huriyya ya kama ragamar mulki a shekara ta dubu karamin lauje da sili da babban lauje al’umma ta shiga halin ha’ula’i. Wannan duk ba wani rikirkitaccen lamari ba ne, matukar a shirye Haurobiyawa suke su fasko wadanda suka yi hada-hadar gwanjon dukiyar kasar nan.
Masana sun yi nuni da cewa kamfanonin kamfatar dukiya sama da daruruwa aka cefanar, al’amarin da ya jefa miliyoyin al’umma a zaman kashe fatari da watangaririya iri-iri a cikin gari. Yau wadanda suka tafka wannan ta’asa sun zo suna ta yi wa jama’a kuri, wai za su CETO ko su CUTAR da kasa?
’Yan makaranta mu himmatu ka’in da na’in wajen karatun kiskali, don faskaren kowane kauli, yadda za mu samu saukin kwance sasarin kowane kulli.
Batu na ingarman karfen karafunan kwangiri layin dogo, ba tare da jan kafar hannayen agogo ba, kowa yasan gyara da wuya, barna na da saukin tsuwururtawa. Matukar dai muna neman mafita, dole ne kowa ya yi kama-kama, har a samu a fice daga duma, mu yi wa nagargarun jagorori mazauni a kan darduma.