Fadar Shugaban Kasa ta ce tsabar raina hankalin ’yan Najeriya ne ya sa wasu sanatoci dauko hayaniyar neman tsige shugaban kasa Buhari.
Kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu ne ya bayyana haka a martaninsa kan barazanar tsige Buhari da ’yan majalisar suka yi idan bai magance matsalar tsaron Najeriya cikin mako shida masu zuwa ba,
- NAJERIYA A YAU: Matsalar Tsaro Za Ta Iya Kawo Wa Zaben 2023 CikasCikas
- Lauyan Abduljabbar ya zargi alkali da hadin baki da gwamnatin Kano
Sanatocin daga jam’iyun adawa na PDP da APGA sun nuna bacin ransu kan yadda Gwamnatin APC ke yi wa tabarbarewar tsaron Najeriya rikon sakainar kashi.
To sai dai wannan batu bai yi wa Fadar Shugaban Kasa dadi ba, domin kuwa a cewarta, wannan batu na sanatocin wasan yara ne kawai.
Sanarwa da Garba Shehu, ya fitar a daren ranar Laraba, ta ce wannan yunkuri na sanatocin da jam’iyunsu ke ta-ta-ta, neman suna ne kawai, don haka watsi da kudirin da Shugaban Majalisar Ahamd Lawan ya yi abu ne da ya dace.
“Madadin kwaikwayon abin da suka gani ana yi a kasar Amurka suna raina hankalin ’yan Najeriya, kamata ya yi su bata lokaci wurin lalubo mafita kan matsalar tsadar kayan abinci da ta shafi kowa a duniya.
“Gazawarsu a yin hakan shi ya sanya za su dawwama a jam’iyun hamayya”, in ji shi.
Ya kuma ce Shugaba Buhari na nan na nemo hanyar da ta fi dacewa wajen magance matsalar tsaron kasar nan, har ma da wanda Jam’iyar PDP ce ta gadar musu a Kudu maso Kudanci da Arewa maso Gabashin kasar.
“Ko kwana guda da ya wuce ’yan matan Chibok biyu sun samu ’yanci daga hannun ’yan Boko Haram, kari kan ukun da aka sako satin da ya gabata”, in ji shi.
Don haka ya ce jam’iyun hamayyar su daina surutan neman suna, domin babu amfanin da hakan zai yi wa kowa, musamman ma al’ummar da suke wakilta.
“Muna maraba da hada hannu da su domin magance matsalolin Najeriya, babu mai maraba da bata lokaci wajen yunkurin tsige shugabn kasa a wa’adinsa na karshe, musamman ma al’ummar da suke wakilta”, in ji Garba Shehu.