Tsohon Fira Ministan Japan, Shinzo Abe, ya rasu bayan an bude mishi wuta wurin yakin neman zabe a safiyar Juma’a.
Mista Abe, wanda shi ne ya fi dadewa a masmtsayin Fira Ministan Japan, ya rasu ne, jim kadan bayan wani matashi ya harbe shi a bainar jama’a a birnin Nara na kasar.
Shinzo Abe, mai shekara 67 ya gamu da ajalinsa ne a yayin da yake tsaka da yakin neman zaben zama dan majalisar dokoki.
- El-Rufai ya nemi a biya N500,000 kafin amfani da filin Idi
- Abubuwa 7 da Ranar Arafa ta 2022 ta zama ta musamman
’Yan sanda sun sanar da kama wani matashi mai shekara 41 kan zargin kai harin.
Fira Ministan Japan mai ci, Fumio Kishida ya ce Mista Abe ya rasu ne a cikin mawuyaci hali.
Rahotanni sun nuna ko da aka garzaya da tsohon Fira Ministan zuwa asibiti bayan an harbe shi, zuciyarsa ta daina aiki.
Harin ya jefa mutane cikin kaduwa da mamaki.