Miguel Oliveira, direben kungiyar Red Bull dan kasar Portugal ya lashe Gasar Tseren Babura na MotoGP Thailand Grand Prix ranar Lahadi 2 ga Oktoba, 2022.
Gasar wadda ita ce ta ta farko cikin shekara uku kasar Thailan ta samu tsaiko sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya a filin tsere na Buriram Circuit.
- Mutum 174 sun rasu, 180 sun jikkata a turmutsutsu a Indoensiya
- Boko Haram ta kashe malaman makarantu 2,295 daga 2009 zuwa 2022
Ruwan ya sa dole aka dakatar da wannan wasan tseren babura da aka shirya farawa karfe 8:00 na safe agogon GMT da minti 55.
Rabon da a gudanar da gasar a kasar tun a shekarar 2019, da aka samu bullar cutar COVID-19, wadda ta kawo tsaiko ga harkoki da dama ciki har da wasanni a fadin duniya.
Baya an samu hasashen yiwuwar samun ruwan sama tun daga ranar Juma’a, amma ba a samu ruwan ba sai ranar Lahadi da aka shirya fara gasar, wanda ya kawo tsaikon da wasan Moto2 da aka shirya.
An shirya wasan zai fara ne da Marco Bezzecchi na kasar Italiya a sahul farko na MotoGP tare da Jorge Martin na kasar Spain da kuma Francesco Bagnaia.
Rabon kasar da gudanar da gasar MotoGP tun shekarar 2019 da aka samu bullar cutar COVID-19.