✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsawa ta lalata gidaje 100 a Filato

Mutanen yankin sun ce an yi tsawar ce babu ruwan sama ko daya

Wata tsawa ta raba kusan mutum 200 da muhallansu a kauyen Mangun da ke Karamar Hukumar Mangu da ke Jihar Filato.

Tsawar, wacce ba a saba ganin irinta ba, ta jefa yankin cikin fargaba, saboda babu ruwan sama lokacin da ta sauka.

Sai dai mazauna yankin sun ce ba a sami asarar rai ko daya ba sanadin tsawar.

Wani mazaunin yankin, Mafulul Ishmael, ya shaida wa Aminiya ta wayar salula cewa, “Mun kirga gidaje sama da 100 da tsawar ta lalata. Lamarin ya wuce duk yadda ake tunani.

“Irin tsawar da na saba gani takan gifta ne a cikin kiftawar ido ta wuce, kuma galibi ana yinta ne lokacin da ake ruwan sama. Amma wannan ita an yi ta ne ba ruwan sama, sannan ta rika bin gidaje daya bayan daya, sannan tana tafiya kamar walkiya,” in ji Mafulul.

Shi ma wani mazaunin kauyen, Samuel Gobum, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce, “Muna tunanin Shaidanu ne suka kawo ta, saboda yadda ta faru ya saba wa tunanin dan Adam. Ba mu taba ganin irinta ba a nan kauyen.”

“Mun ji labarin an yin ruwan sama a wasu sassan Jihar nan, amma ba a yi a Mangun ba, abin da kawai muka gani ita ce tsawar da ta tasam ma halaka liahirin kauyenmu, ciki har da makarantarmu ta Firamare,” in ji wani mai suna Andrew Daspan.

Sai dai duk kokarin wakilinmu na jin ta bakin Shugaban Karamar Hukumar ta Mangu, Minister Daput, ya ci tura, saboda bai daga wayarsa ba, kuma bai kira ba, har zuwa lokacin hada wannan rahoton.