✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ruwan sama ya lalata aƙalla gidaje 70 a Filato

Mamakon ruwan sama da aka yi a daren Laraba, wanda ya biyo bayan ruwan sama, ya yi ɓarna matuƙa a unguwannin.

Sama da gidaje 70 ne suka lalace da rumfuma a wata guguwa da ta yi ɓarna a unguwar Mabudi, Sabon Gida, da sauran unguwanni a ƙaramar hukumar Langtang ta Kudu a Jihar Filato.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, mamakon ruwan sama da aka yi a daren Laraba, wanda ya biyo bayan ruwan sama, ya yi ɓarna matuƙa.

Mazauna yankin sun shaida wa wakilinmu cewa kimanin gidaje 70 ne rufinsu ya ɗaga, yayin da wasu gine-gine suka ruguje.

Nanbol Nanzing, wani mazaunin ɗaya daga cikin unguwar da lamarin ya shafa, ya koka da yadda lamarin ya faru tare da yin kira ga gwamnatin jihar ta tallafa.

Shugaban ƙaramar hukumar Langtang ta Kudu, Hon. Nanfa Nbin ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Mista Iliya Bako.

A cewar sanarwar, kwamitin bayar da agajin gaggawa na Ƙaramar hukumar Langtang ta Kudu, wanda shugaban Ƙaramar hukumar ya kafa, ya ziyarci gidajen da lamarin ya shafa domin jajantawa waɗanda lamarin ya shafa.