Mutum 11 da suke daukar hoton ‘selfie’ ne suka rasu, wadansu da dama kuma suka jikkata bayan da wata tsawa ta auka wa wani muhimmin ginin tarihi a kasar Indiya.
Kimanin mutum 30 ne suke cikin hasumiyar ginin na Amer Fort da aka gina a Karni na 12 a birnin Jaipur, babban birnin Rajasthan lokacin da tsawar ta auku.
- ‘Babu wanda ya fi shiga matsalar tsaro kamar manoma’
- An gurfanar da mahaifin da ya kai wa ’ya’yansa cafka a mama
Mutum 17 sun jikkata, yayin da uku daga cikinsu suke cikin mawuyacin hali, inji ’yan sandan yankin.
Ginin wanda ke da kyan gani a birnin Jaipur, ya cika da masu yawon bude-ido ranar da bala’in ta auku.
Mutane suna tsaka da daukar hotunan salfi a kusa da hasumiyar ginin ne, lokacin da tsawar ta auku a kusa da ginin Amer, inda wadansu suka yi tsalle zuwa kasan ginin bayan jin karar tsawar, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka ruwaito.
Babban jami’in ’yan sandan birnin Jaipur, Mista Saurabh Tiwari ya ce: “A lokacin da aka yi tsawar ana ruwan sama ne kuma mutane sun yi taru a hasumiyar yayin da ruwan ya tsananta.
“An bar wadansu daga cikin wadanda suka jikkata a sume sakamakon aukuwar tsawar.
“Wadansu kuma sun firgita tare da samun munanan raunuka.”
Ayarin masu ba da agajin gaggawa sun isa wurin, inda suka duba ko wadanda abin ya shafa sun fada a wani rami mai zurfi a wani bangare na ginin.
Daruruwan mutane ne ke mutuwa a Indiya kowace shekara sakamakon tsawa a farkon lokacin damina.
Firayi Ministan Indiya, Mista Narendra Modi ya ce, za a biya diyya ga iyalan mutanen da suka rasa rayukansu, yayin da ya jajanta wa wadanda lamarin ya shafa.
Ofishin Firayi Ministan ya wallafa a shafinsa na Tiwita cewa: “Za a bai wa dangin mamatan Rupin kasar dubu 200 (daidai da Naira miliyan daya da dubu 79 da 204) yayin da za a bai wa wadanda suka jikkata Rupi dubu 50, (daidai da Naira dubu 269 da 801).”
Hukumar Hasashen Yanayi ta Indiya ta yi gargadin yiwuwar kara samun tsawa a cikin kwanaki masu zuwa a yankin.