‘Yan Sanda a jihar Adamawa sun tabbatar cewa tsawa ta kashe masu garkuwa 18 a Jamhuriyar Kamaru mai makwabtaka da Najeriya.
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Adamawa ta tabbtar da hakan ne yayin karyata rahotannin da ke cewa tsawar ta kashe masu garkuwa da mutanen ne a Karamar Hukumar Tungo da ke jihar.
“Abin ya faru ne a jejin Pawati a Jamhuriyar Kamaru. Babu wani abu kamar haka da ya faru a fadin Tungo kamar yadda ake rade-radi”, a cewar SDP Suleiman Yahaya Nguroje.
- ‘Yan sanda sun kashe gungun ‘yan fashi a musayar wuta
- Kaduna ta fadada dokar kukken Zangon Kataf da Kauru
DSP Suleiman wanda shi ne Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda a Adamwa ya ce rufe iyaka da aka yi tsawon lokaci ya hana bata-gari tsallakowa zuwa jihar ta Adamawa.
Ya kuma bukaci jama’a su yi watsi da rahoton da ke cewa a Tungo tsawar ta kashe masu garkuwa da mutanen.
Karamar Hukumar Tungo da ke jihar Adamawa a Najeriya ta yi iyaka da Jamhuriyar Kamaru.