✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsare-tsaren Tinubu Da Suka Gigita ’Yan Najeriya a Shekara 1

A shekara ɗaya gwamnatin Tinubu Bola ta bullo da tsare-tsare sannan ta dauki wasu matakai suka haifar da ce-ce-ku-ce a Najeriya.

A shekara ɗaya na mulkin Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasar Najeriya, gwamnatinsa ta kaddamar da wasu tsare-tsare da suka haifar da ce-ce-ku-ce a kasar.

Wadannan tsare-tsare da matakai masu cike da rudani da gwamnatin ta aiwatar sun hada da wadannan:

Ga wasu daga cikinsu:

1. Cire Tallafin Mai

A ranar 29 ga Mayun 2023  Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur, a cikin jawabinsa na kama aiki matsayin shugaban kasa.

Wannan furuci ya gigita ’yan Najeriya, domin take man fetur da ake sayar da lita guda a kan Naira 200 zuwa 250 ya yi tashin gwauron zabo ya koma tsakanin Naira 450 zuwa Naira 500.

Tun daga wannan lokaci harkar sufuri da masana’antu da ma tattalin arziki kacokan suka shiga matsala sakamakon hauhawar farashi da tashin farashin man ya jefa miliyoyin al’unmar kasar.

Sai dai kamar yadda ya ce, babu wata zanga-zanga da za ayi da za ta sa shi ya dawo da tallafin man fetur.

An yi zanga-zanga a yankuna da dama na kasar nan, kungiyoyi kwadago sun shiga yakin aiki domin a dawo da tallafin amma har yanzu shiru.

2. Karin Kudin Lantarki

Soke tallafin wutar lantarki na daga cikin matakan da gwamnatin Tunubu ta dauka da har yanzu suke jawo mata Allah wadai daga al’ummar Najeriya.

A ranar 3 Afrilun 2024 ne kwamishinan hukumar wutar lantarki (NERC) Yusuf Ali  ya sanar da kara farashin wutar lantarki.

Ninka kudin kilowatt daya na lantarki da NERC ta yi daga N66 zuwa N225 ya jawo maganganu kafin majalisar dokoki ta kasa ta ba da umarnin ragewa.

Wani abin da ya fi jawo suka shi ne rarraba masu amfani da wutar da kamfanonin rarraba wutar suka yi, ta yadda wadanda ke kan layin Band A suke da tabbacin samun wutar akalla awa 20 a kullum, sauran layukan kuma sai abin da aka ba su.

A karshe NERC ta sanar da rage farashin da Naira 19 a kowane kilowatt, wanda bai gamsar da al’umma ba.

Wannan kari da aka yi ya janyo wa Bola Ahmed Tinubu zagi, kasancewa a karkashin gwamnatinsa aka yi wannan kari tashi ɗaya.

3. Karin Jarin Bankuna

Wani sabon tsarin da ya jawo maganganu shi ne umarnin Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya kara mafi karancin uwar kudin bankuna zuwa Naira biliyan 500 ga bankuna masu huldar kasa da kasa.

Masu hulda a fadin kasar kuma Naira biliyan 200, sai masu gudanar da harkoki a yankuna kuma biliyan 50, sai bankuna marasa karbar kudin ruwa, biliyan 20 ga masu harka a fadin kasa sai biliyan 10 ga na yankuna.

Rabon da a kara a uwar kudin bankuna a Najeriya tun 2005, lokacin da CBN ya jara daga biliyan biyu zuwa biliyan 25 lamarin da ya kai ga raguwar bankunan kasar daga 89 zuwa 24.

Duk da ce-ce-ku-ce, masana sun bayyana cewa karin zai kara wa bankuna karfi da kuma ba da tabbaci ga masu ajiya.

4. Karin Kudin Fito

Yawan ƙarin kudin fiton kayan da aka shigo kasashen ketare na daga cikin abubuwan da suka dagula wa ’yan Najeriya.

Karin kudin da aka yi a sakamakon tashin Dala ya yi sanadiyar hauhawar farashin kayan masana’antu da ma na masarufi.

A shekara guda na mulkin Tunubu hukumar kwastam ta kara farashin kudin fito akalla sau 30.

A wata uku na farkon 2024 kadai an kara kudin sau 28, inda a watan Janairu kadai aka kara sau 15 sakamakon tashin farashin canjin Dala.

5. Bashin Kudin Karatu

Shugaba Tinubu a bayanin godiya ga ’ya’yan jam’iyyarsa bayan an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben takarar kujerar shugaban kasa a  2023, ya bayyana cewa zai fito da tsarin bayarvda rancen karatu ga daliban Najeriya da suka fito daga gidaje masu kananan karfi.

Dalibai da iyayensu sun yi murna, sai dai kash! Murnar ta koma ciki ganin irin matakan da aka saka na karɓar rancen.

Wasu na ganin babu mai iya cika l ƙa’idoji da aka gindaya, musamman inda aka ce wajibi ne mahaifi ko wanda ke daukar nauyin karatun dalibin ya kasance ba ya iya samun abin da ya kai Naira dubu 500 a shekara.

Da kuma wadanda za su tsayawa mutum a matsayin wakilai.

5. Karin Kudin Ruwa

A shekarar 2024 kaɗai, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kara kudin ruwa har sau uku.

A watan Fabrairu ana biyan kashi 18.75 sai aka mayar da shi 22.75.

Sai aka kara dagawa daga 22.76% zuwa 24.75%

Daga 24.75 a cikin Maris kudin ruwa ya karu zuwa kaso 26.75 a watan Mayu.

Wannan kari da ake samu duk da cewa ba kai-tsaye yake fitowa daga fadar shugaban kasa ba, ana alakanta shi da shugaban, kuma yana ci gaba da janyo masa ce-ce-ku-ce a tsakanin al’ummar kasar.

6. Harajin Tsaron Intanet

A karshen watan Afrilu babban Bankin Najeriya (CBN) ya umurci bankunan kasuwanci su fara cirar kaso 0.5% na duk kuɗin da aka tura ta intanet a matsayin harajin tsaron kafar.

’Yan kasar sun yi ca a kan labarin kuma suka yi sa’a, wannan doka ba samu nasarar fara aiki ba.

Wannan tsari da aka nemi fito da shi ya dagula hankalin ’yan Najeriya inda a karshe Tinubu ya umarci babban bankin ya jingine shi.

7. Motoci Masu Amfani da Iskar Gas

Tinubu ya ba da umarnin daina  sayen motoci masu amfani da iskar gas dukkan ma’aikatu da hukumomin gwamnati a koma masu amfani da iskar gas.

Sai dai wani bincike da muka gudanar ya nuna cewa jihohi 10 ne kacal cikin 37 har da Abuja suke da cibiyoyin canza motoci masu shan fetur su koma amfani da gas.

Kazalika ’yan Najeriya na kokawa kan karancin wuraren da za su je a mayar da motocinsu masu amfani da gas din da ake kira CNG, ga shi kuma babu tashohin da dura gas din kamar yadda ake da na man fetur.

8. Yanke Wutar Nijar Daga Najeriya 

A watan Agustan 2023 Tunubu ya rufe iyakokin Najeriya da Nijar da nufin matsa lamba ga sojojin da suka hambarar da Shugaba Mohammed Bazoum su mika mulki.

Matakin dai ya taba harkokin kasuwancin kasashen biyu, ta yadda har magani ya zama ba a iya shigar wa Nijar daga Najeriya.

Najeriya ta yanke wutar lantarkin da kasar ke ba wa Nijar, a matsayin biyayya ga umurnin kungiyar ECOWAS na yanke hulda a Nijar saboda juyin mulkin.

Shugaba Tinubu ne dai shugaban kungiyar shuwagabannin kasashen Afrika ta yamma, wato lEOCWAS ko CEDEAO.

’Yan Arewacin Najeriya da masu sharhi kan al’amuran yau da kullum sun soki lamirin ECOWAS na neman amfani da karfi soji wurin sasanta shuwagabannin kasar Nijar, bayan sojoji sun yi wa Shugaba Mohammed Bazoum juyin mulki.

Sanin cewa akwai alaka mai karfi tsakanin ’yan Najeriya, musamman Arewacin kasar, matakin ya janyo wa Shugaba Tinubu tsangwama da raguwar masoya a siyasance.

9. Mayar da CBN Legas

A watan Janairu na 2024 babban bankin Najeriya ya mayar da wasu sassansa daban-daban da ma’aikatansu 1,533 Jihar Legas.

Wannan mataki ya sa ’yan Najeriya da dama yarda da jita-jitar cewa Tinubu na shirin mayar da fadar shugaban kasa Legas, mahaifarsa.