Mu sha biyar daidai,
A Gidan Makama dai,
Sai shugaba sai dai,
Ba mu je da shi din ba.
Kafin mu dau hanya,
Sai shugaban tafiya,
Mai unguwar shiyya,
Ya kira mitin babba.
Bayan mitin din nan,
Mun fiffito din nan,
Wasu na ta saurin nan,
Ba mu aje kowa ba.
Mun hau cikin mota,
Tafiya mun fara ta,
Wasu na ta ratata,
Wasu ba su fara ba.
Mun keta dan daji,
Sai ga mu Bebeji,
Mun hangi ’yan kaji,
Ba mu je da kunci ba.
Mun jera motoci,
Sun ba mu butoci,
A cikin ’yan mintoci,
Ba mu yo da sauri ba.
Mun sauka Bebeji,
A wayarmu full caji,
Wasu ma da ’yan canji,
Ba mu nuna sauri ba.
Bayan da an daura,
Sai hotuna sura,
Kowa yana shukura,
Su alawa anka raba.
Yau Shehu Bebeji,
Da ya samu ’yan canji,
Sai ya zaga Bebeji,
Bai dau ta wasa ba.
Ya zabi ’yar kirki,
Ita za ta mai girki,
Ita ce uwar daki,
Ba ta zo da wargi ba.
Bayan da mun kimtsa,
Bakinmu ya motsa,
Lemu fa mun tsotsa,
Ba mu kyale waina ba.
Mun gabji Dambu ma,
Kifi kanin nama,
Figo fa ya tsama,
Bai ragge kifi ba.
Bayan da mun koshi,
Na ji Koki na nishi,
Su Bajjatu an koshi,
Bai kyale komai ba.
Bayan da mun gyatse,
Muka je hawa dutse,
Mu ka hau sama a natse,
Sheshe yana a gaba.
Kamfarrawa dutse,
Mun haushi duk a natse,
Dutsen fa ya batse,
Ba mu hau da wasa ba.
A hanya ta dawowa,
Na ga masu toyawa,
Wata waina son kowa,
Sunan ban gane ba.
Wai kun ji sunanta,
Alasara sunanta,
A zubi da tsarinta,
Ba ta kai ta waina ba.
Su dai Alasawa,
Tushensu ’yan baiwa,
Bebeji ce aiwa,
Tarihi bai buya ba.
Sun gyara wanga gari,
Sun fidda duk tsari,
Tushe abin fahari,
Ba su bar kazanta ba.
Nan za ni dan huta,
Tsaraba da na yi ta,
Allah Ka ban mafita,
Na zamo uba a gaba.
Ibrahim Hamisu ne,
Ashirin da ma daya ne,
Tsaraba na tsara ne,
Mu hade jiko na gaba.