✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsananin neman mijin aure ya sa tana tallar kanta a titi

Ina neman mijin da ke tsakanin shekara 20 zuwa 70.

Wata mata da take tsananin son aure ta fita kan titunan Tanzaniya tana neman mijin aure, inda take cewa shekaru ba sa cikin tsarinta.

A wani bidiyo da aka wallafa a YouTube, an ga matar dauke da wani allo mai rubutu a yankin Buza da ke birnin Dar es Salaam na kasar Tanzaniya.

A jikin allon an rubuta cewa: “Ina neman mijin da ke tsakanin shekara 20 zuwa 70.”

Lokacin da take magana a kafar YouTube ta Tanzaniya, matar ta ce za ta biya sadakinta kuma ta yi ikirarin cewa, har yanzu ita budurwa ce.

“Har ma na tanadi zoben aure tare da ni.

“Zan biya sadaki har ma in sayi suturar ranar biki ga angon da zai aure ni, muddin yana da mutunci da tsoron Allah,” inji matar wadda take sanye da rigar aure don neman miji.

Ta ce, an tilasta mata ta dauki matakin da ya dace, saboda gudun kada lokaci ya kure mata ba tare da ta yi aure ba.

Don haka, ta yanke shawarar sayen suturar aure kan kudin Tanzaniya KSh 142,000 (daidai da Naira dubu 531, 185).

“Ina kara tsufa kuma ina bukatar namiji a tare da ni. Ban karya doka ba, don na yi hakan, ina da karfin gwiwa.

“Wannan shawara ce ta kashin kaina kuma babu wanda zai iya yanke min hukunci,” inji ta

Ta nanata cewa, tana da kudi sosai kuma tana neman mutumin da zai so ta da aure.

“Ina da kudi, ba na son in wahalar da mijina, zan yi amfani da kudina wajen gudanar da wasu harkokina,” inji ta

Ta ca ba wannan ne farau ba da take bi kan tituna don neman mijin aure.