Likitoci sun cika da mamakin ganin wata yarinya wadda tsakuwa ke fitowa daga idonta a maimakon hawaye.
Budurwar mai shekara 15 ta zama babban abin al’ajabi ga fannin likitanci, duk da cewa likitocin ta suka duba ta sun ce lalaurar da take fama da shi abu ne da ba zai taba yiwuwa ba a likitance.
- Mafarauci ya tsinci kayan tarihi mai shekara 6,000 a cikin kada
- Matar da ta shekara 40 ba ta yi barci ba
An shafe kusan watanni biyu ’yan uwan budurwar, daga yankin Kannauj na Jihar Uttar Pradesh da ke Arewacin kasar Indiya, suna ikirarin cewa kananan duwatsu 10 zuwa 15 na fitowa daga idonta na hagu.
A wani bidiyo da aka dauka a kauyen Gadiya Balidaspur, ana iya ganin wani kullutu mai kama da tsakuwa a saman idonta na hagu.
An kuma ga wani daga gefe yana tausa idon budurwar, sai wani abu mai kamda da dutse ya fito daga marfun idonta na kasa, ya fado a saman rigarta.
Daga bisani kuma wani abu mai kama da taskuwa ya sauko ta sama daga daya bangaren dama na idon nata na hagu.
A wannan karon, tsakuwar ta sauko ne daga kusa da bututun hawayenta kafin ya sake faduwa, inda aka ga wata mace ta tare shi a cikin tufafinta.
Daga nan sai yarinyar ta rike tsakuwar a hannunta, sannan ta nuna wani tarin tsakuwa da take ikirarin cewa daga kwayar idonta suka fito.
Iyalin yarinyar dai sun tuntubi likitoci ne domin yi mata magani, amma dukkannin likitocin sun dage cewa matsalar da aka zo musu da ita abu ne da ba zai yiwu ba a likitance.
– Ba yanzu farau ba
Karo na biyu ke nan da aka samu mai irin wannan lalurar ta fitowar tsakuwa daga kwayar ido.
A shekarar 2014, kafar Mail Online ta ba da rahoton wata yarinya mai shekara 12 mai suna Sa’adiya Saleh, ’yar kasar Yemen, wadda take fama da irin wannan yanayin.
Likitoci sun ce har yanzu ba za su iya ba da bayani kan irin wannan yanayin ba tunda ita Sa’adiya Saleh ba ta fama da wata cuta da aka sani.
Hakan ya haifar da fargaba a kauyen su Sa’adiya, inda wasu ke zargin sihiri aka yi mata.
A wani bidiyon YouTube da gidan talabijin na Azal na kasar Yemen ya nuna, an ga likitoci dauke da wani karamin akwati da duwatsu a ciki, wadanda suka ce sun fado ne daga idanun Sa’adiya.
An ji mai gabatarwan yana cewa: “Wannan abun al’ajabi shi ne irinsa na biyu a yankin. Abun ya haifar da fargaba a zukatan mazauna yankin da wannan yarinyar ke zaune…
“Wasu na cewa abun ya yi kama sihiri, wasu kuma na cewa mai yiwuwa jifa ce, wasu kuma na fargaba cewa hakan na iya zama farkon barkewar annoba.”