Rediyo da jarida na daga cikin kafafen sadarwa da ke taimakawa wajen fadakarwa da aika sako ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, tsakaninsu, wacce ya fi tasiri? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suka kalato mana:
Rediyo ya fi jarida muhimmanci
– Maikudi Audu
Maikudi Audu Yola: “Rediyo ya fi jarida isar da sako domin jarida ba kowa ne ya iya karanta ta ba. Amma rediyo ga sji nan a hannun mutane a cikin birane da kauyuka na kasashen duniya daban-daban suna sauraron labarai da dumi-duminsu. Shi ma wanda bai iya karatu ba yana sauraron rediyo. Saboda haka nake ganin rediyo ya fi jarida tasirin isar da sako ga jama’a.”