A yau ina so ku ba ni dama domin in tofa albarkacin bakina game da kulli-kurciyar da ake ci gaba da yi tsakanin tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo da gwamnatin Shugaba Buhari, inda Obasanjo ke kai wa gwamnatin hari ido rufe ita kuma tana karewa. Da farko dai idan muka kalli abin ta fuska biyu, abu na farko shi Obasanjo ya hau tudun nan da ake kira na laifi, wanda za ka take naka ka hango na wani. Kazalika tsohon Shugaban yana amfani da kiyayya da bi-ta-da-kullin siyasa har sai ya shafa wa gwamnatin Buhari kashin kajin da ’yan Najeriya za su ji warinsa su kyama ce ta, duk kuwa da makarar da ya tafka ta yin haka.
A daya gefen kuma gwamnatin Shugaba Buhari da jam’iyyarsa da sauran magoya bayansa ba sa ga maciji da juna da duk wani da zai daga baki ya ce ga inda gwamnatin ta yi ba daidai ba, saboda tsabar son zuciya da makauniyar soyayya da wadansu jama’a ke yi wa Shugaba Buhari. Wannan ya taka rawa ainun wajen kasa hango matsalolin da suka dabaibaye gwamnatin.
A karshe mafita daya tilo ce ta rage wa mu talakawan Najeriya, mu dukufa da addu’a kafin mu bayyana a gaban akwatunan zabe gobe domin zabar shugabanninmu.
Ya Allah Ka ba mu shugabanni nagari masu kishinmu da kuma kasarmu, ba ’yan je-ka-na-yi-ka ba. Amin ya rabbil alamin.
Daga Ashiru Lawal Nagoma Ruwan Ɓaure, Jihar Zamfara. 07086868025.