✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsakanin karin kudin lantarki da na man fetur, wanne ya fi matsala ga al’ummar kasa?

Lantarki da man fetur suna daga cikin mafiya muhimmanci ta fuskar makamashi ga al’ummar kasa. Abin tambaya a nan shi ne, idan aka kara musu…

Lantarki da man fetur suna daga cikin mafiya muhimmanci ta fuskar makamashi ga al’ummar kasa. Abin tambaya a nan shi ne, idan aka kara musu farashi, wanne daga cikinsu zai fi jaza matsala ga al’umma? Wakilanmu sun tattauna da mutane kuma ga abin da suke cewa:

karin farashin fetur na jawo kunci – Musa Lar

Hamza Aliyu, a Bauchi

Alhaji Musa Adamu Lar: “Abin da zan fada game da wannan tambaya shi ne kara kudin man fetur da kara kudin wutar lantarki wanda ya fi shafar al’umma kai tsaye shi ne man fetur, domin sama da kashi 85 cikin 100 na rayuwar ’yan Najeriya kusan kowa yana amfani da man fetur. Akwai dimbin mutane wadanda suke zaune a karkara, babu ruwansu da wutar lantarki amma suna da kananan janareta wadanda ke amfani da man fetur. Da wahala ka shiga kauye ka ga babu wanda yake da babur ko mota ko injin nika da sauran abubuwan da suke amfani da man fetur. Kamar yadda Shugaban kasa ya fada abin da ya jawo kara kudin wutar lantarki shi ne sai da kamfanin da aka yi ga ’yan kasuwa don haka suka kara kudin wuta. Muna da kauyuka masu yawa a karamar Hukumata ta Tafawa balewa wadda ba su da wutar lantarki amma suna amfani da man fetur. Da yawa daga cikin mutane ba su damu da kara kudin wutar ba amma dai idan an kara kudin ya kamata a rika samun wutar a kowane lokaci.”

Farashin fetur ya fi matsala – Rulwanu Ibrahim

Hamza Aliyu, a Bauchi

Alhaji Rulwanu Ibrahim Katsinawa: “A gaskiya abin da zan fada game da amsar wannan tambaya shi ne kara farashin man fetur da kara kudin wutar lantarki wanda ya fi shafan talaka kai tsaye shi ne man fetur kuma ya kamata a fahimci cewa amfanin wutar lantarki kadan ne a wajen al’umma. Duk lokacin da aka kara kudin man fetur kusan komai sai ya yi matukar tsada, abin da za ka saya Naira goma idan aka kara kudin man fetur sai ka saya Naira talatin. A matsayina na shugaban masu sai da doya na Jihar Bauchi, duk lokacin da aka kara kudin man fetur, masu kawo mana doya sai sun kara kudin mota. Man fetur ya shafi kowa da kowa a Najeriya kuma akwai dimbin mutanen karkara wadanda babu ruwansa da wutar lantarki.”

karin farashin fetur ya fi illa – Buhari Sakatare

Bashir Yahuza Malumfashi, a Abuja

Alhaji Buhari Ibrahim Sakatare: “Ni a ra’ayina kuma a fahimtata, karin farashin fetur shi ya fi muni da illa ga al’ummar kasa, musamman saboda dalilaina kamar haka: Shi man fetur ya shafi rayuwar al’umma gaba daya. Idan aka kara farashin mai, zai shafi abin da ya danganci samarwa da hauhawar farashin kayan abinci da ma dukkan daukacin kayan masarufi da suka shafi kowane talaka. Harkar sufuri ma za ta shiga matsala, musamman za a samu karin farashin zirga-zirga, wanda haka zai shafi al’umma ta wajen kawo kunci da matsi. Muhimman sassa kamar noma, kasuwanci, aikin gwamnati da sauransu duk za su canza, wanda haka zai shafi dukkan al’ummar kasa. Haka kuma, idan mun lura, ita kanta wutar lantarkin, ai sai da mai take samuwa, tun da injina da sauran na’urorin da ake amfani da su wajen samar da wutar, suna amfani da fetur ko dizal ko iskar gas. Don haka dai, karin farashin man fetur shi ya fi illa da kawo matsala ga al’ummar kasa fiye da na wutar lantarki.”

Farashin wuta ya fi illa – Nasiru Ahmad

Bashir Yahuza Malumfashi, a Abuja

Nasiru Ahmad Labbo: “Ni dai a fahimtata, karin farashin wutar lantarki ya fi matsala da jawo illa ga al’umma, musamman saboda ganin cewa a rayuwarmu ta yau da kullum, babu abin da bai shafi wutar lantarki ba. Idan muna maganar sarrafa abinci da samar da shi, koyarwa a makarantu, harkar sufuri, kasuwanci da sauran al’amuran rayuwa, duk sun ta’allaka da wutar lantarki. Ruwan sha, abu ne mai matukar muhimmanci ga al’umma, domin idan babu ruwa, kusan a iya cewa babu rayuwa kwata-kwata kuma lallai da wutar lantarki ce ake amfani wajen tace shi da samar da shi ga al’umma. Don haka idan farashinta ya tashi, farashin komai ma zai tashi, wanda hakan kuma babbar illa ce ga al’umma, musamman ma talakawa da ba su da harka.”

karin farashin fetur ya fi matsala – Yusuf Suleiman

Sani Gazas Chinade, a Damaturu

Malam Yusuf Suleiman: “A ganina tsakani da Allah, karin farashin kudin man fetur shi zai fi addabar al’umma fiye da karin farashin wutar lantarki. Dalilina na fadar haka kuwa shi ne, ai mafi yawan hanyoyin da talakawan kasa ke bi don neman abincinsu da duk wata walwalarsu da man fetur suke amfani. Don haka mu al’ummar kasa, kara farashin mai shi ne babbar matsala fiye da kara farashin wuta; tunda ai ita wutar lantarki sai mai sukuni, sabanin man fetur a matsayin na kowa.”

karin farashin fetur ya fi daga hankali – Musa Adam

Sani Gazas Chinade, a Damaturu

Musa A. Adam: “A ganina, tsakanin karin kudin man fetur da karin farashin kudin wutar lantarki, wanda zai fi kuntata rayuwar al’umma fiye da kima shi ne karin kudin man fetur. Dalilina na fadar haka kuwa shi ne, ai ita kanta wutar lantarki ba kowane mutum ne ke iya amfani da ita ba, to amma man fetur kuwa na kowa ne. Don haka karin farashin man fetur shi zai fi kuntata rayuwar al’umma, domin karin farashin na mai babbar annoba ne ga kasa da al’ummarta.”