✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsagerun Neja-Delta sun sun kai wa ’yan sanda hari

Rundunar ’yan sandan Jihar Ribas ta bayar da sanarwar harin da tsagerun yankin Neja Delta suka kai wa jirgin ruwan jami’anta mai dauke da mutum…

Rundunar ’yan sandan Jihar Ribas ta bayar da sanarwar harin da tsagerun yankin Neja Delta suka kai wa jirgin ruwan jami’anta mai dauke da mutum shida, mutum biyar sun bace a wani kwanton bauna da  tsagerun  suka yi, lokacin da suke bakin aikin sintiri a zirin tekun Okujagu, karamar Hukumar Okrika.
DSP Ahmad Muhammad, jami’in hulda da jama’a na rundunar ne ya sanar wa manema labarai afkuwar hakan. Ya ce: “Rundunar ’yan sandan Jihar Ribas tare da wasu abokan aiki sun yi batan dabo a wani kwanton bauna da ’yan bindiga suka yi masu, yayin da suke gudanar da aikinsu a kauyen Okujagu. Wasu da ba a san ko su waye ne ba suka aikata wannan danyen aiki.” Inji sanarwar.
Ya ce biyu daga cikin ’yan sandan masu mukamin sufeto ne sauran hudu kuma kurata ne amma sanarwar ta ce an yi katarin kubutar da wani sufeto mai suna Aferuan Imoukhuede. Kawo yanzu rundunar ta ce ta kama mutane 55 da take zargi da hannu wajen aiwatar da laifin.