A yayin da daminar bana take gabatowa, wani Malami a Tsangayar Koyar da Dabarun Noma da ke Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, Farfesa Salihu Adamu Dadari, ya yi hasashen cewa bisa dukkan alamu noma zai ragu a daminar bana sakamakon tsadar taki da maganin feshi da sauran kayan aikin gona.
Malamin, ya yi wannan hasashen ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya.
- 2023: Osinbajo ya sayi fom takararsa a APC na N100m
- An ba maniyyata kwana 7 su gama biyan kudin kujerar Hajji
Ya ce, babu shakka a daminar bana, akwai alamun matsaloli masu tarin yawa musamman kan tsadar taki da maganin feshi.
Domin buhun takin Kamfanin NPK da ake sayensa a bara kan kudi Naira dubu 12, zuwa Naira dubu 15, bana ana sayar da shi kan Naira dubu 25 zuwa Naira dubu 30, a yayin da buhun takin Urea da ake sayarwa a bara Naira dubu 9, zuwa Naira dubu 10, bana ana sayar da shi Naira dubu 17, zuwa Naira dubu 18.
Shi ma farashin maganin feshi, a bana ya ninka kan farashin shekarar bara.
Malamin, ya yi bayanin cewa babban abin da ya kawo wannan matsala shi ne karyewar darajar kudinmu, wanda miyagun shugabanni suka kawo mana.
Ya ce, tunda wannan gwamnati ta yi kira kan a koma noma, kuma jama’a sun amsa wannan kira, ta yi kokari ta
magance wannan matsala ta hanyar kawo wa manoma taki da maganin feshi a farashi mai rahusa, domin dorewar nasarar da ta samu kan aikin noma.
“Dole ne mu yi noma, mu samu abincin da za mu ci ko gwamnati ta tallafa mana ko ba ta tallafa mana ba. Don haka muna kira ga manoma idan ba su iya noman hatsi ba saboda tsadar taki da maganin feshi su yi kokari su noma dankali ko gwaza ko waken soya.” Inji Farfesa Salihu.