Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa, Alhaji Umar Iliya Damagum, ya bayyana cewa ’yan Nijeriya da suka karbi taliya da atamfa a lokacin zaben shugaban kasa na 2023 sun fi kowa shan wahalar matsin tattalin arziki a halin yanzu.
Damagum ya bayyana hakan ne a lokacin da ya amsa tambayoyin manema labarai a ranar Juma’a a ziyarar da ya kai wa Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na jihar Bauchi.
Mukaddashin shugaban jam’iyyar ya kai ziyarar ne a wani bangare na kokarin magance matsalolin da rikicin cikin gida da jam’iyyar ke fuskanta a halin yanzu.
Damagum ya ce galibin ’yan Nijeriya suna ci gaba da fuskantar wahalhalu sakamakon manufofin Shugaba Bola Tinubu na Jam’iyyar APC.
- Ya zama dole Tinubu ya dawo da tallafin man fetur — Obi
- Son zuciya ne ya haifar da koma-bayan dimokuraɗiyya a Nijeriya – Sani GNPP
A cewarsa, “Jam’iyyar APC ba ta da wani shiri na gudanar da mulki, to ta yaya kuke tsammanin wani alheri zai fito daga gare su?
“Wadanda suka karbi taliya da atamfofi don kawo wannan gwamnati suna jin zafinta fiye da kowa.
“Kuma wannan ya kamata ya zama darasi ga dukkanmu cewa ya kamata mu nemi gaskiya, wadanda aka tabbatar za su iya mulki kuma an gwada su, wadanda suke shirye su yi mulki su ya kamata mu zaba,.” in ji Damagum, wanda ya ce ’yan Nijeriya suna koyon darasi mai daci.
Damagun, wanda wani bangare na Kwamitin Ayyuka na Kasa (NWC) na Jam’iyyar PDP tare da Sakataren Jam’iyyar na Kasa, Samuel Anyanwu, suka dakatar da shi bisa zargin rashin biyayya ga jam’iyyar, ya zargi wani bangare na ’yan Nijeriya da makanta ta hanyar karbar kayan abinci a lokacin da za a zabi Shugaba Bola Tinubu.
Da yake magana kan ziyarar Damagum a Jihar Bauchi, Gwamna Bala Mohammed, wanda shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP ya musanta cewa akwai wani bangare a PDP.
Gwamna Mohammed ya ba da tabbacin cewa za a warware dukkan matsalolin da suka shafi dakatarwa da rigingimu a cikin jam’iyyar cikin ruwan sanyi.