Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya tunatar da ’yan Najeriya cewa hanya mafi dacewa domin samun sauki daga wahalhalun da ake fama da su a kasar ita ce komawa ga Allah da addu’a.
Sarkin Musulmi ya jaddada muhimmancin shugabanni su yi adalci, sannan ya bayyana cewa, wahalhalun da ake fama da su a kasar a halin yanzu sun samo asali ne daga kaucewar da mutane daga tafarkin Allah, domin haka dole a koma ga Allah domin Shi ke da mafita.
Ya ci gaba da cewa, “Kowa ya san halin da Najeriya ke ciki a halin yanzu, amma mafita ita ce mu koma mu nemi dauki daga Allah, amma ba da da addu’o’i na gaskiya ba don riya ba, domin Allah Ya ce duk tsanani na tare da sauki.”
Sarkin yi a ci gaba da cewa, wahalhalun da ake fama da su a kasar a yanzu sun samo asali ne daga kaucewar da mutane daga tafarkin Allah.
- An kama fasto kan safarar yaran Arewa zuwa kudancin Najeriya
- Yadda beraye suka tilasta wa manoma kwana a gonakinsu a Kano
“Duk wanda ya bar yin da’a ga Allah to tabbas Allah Zai rabu da al’amarinsa, hakan ya tabbata a wurare da dama a cikin Alkur’ani Mai Girma,” in ji shi.
Sarkin Muslumi ya yi wannan kiran ne a Abuja ranar Juma’a a wajen taron bude y na Masallacin Juma’a wanda hedikwatar Jama’atu ta Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa’kamatis Sunnah (JIBWIS) ta gina.
Wakilin Sarkin Musulmi a bikin kuma tsohon sakataren gwamnatin tarayya Alhaji Yayale Ahmed, ya taya shugaban JIBWIS murnar samun nasarar kammala aikin masallacin da yin alkawarin ci gaba da bayar da gugunmawa domin ganin an kammala cibiyar ta addinin musulunci da ke wurin.
Sarkin Musulmi ya jaddada muhimmancin shugabanni su yi adalci da kuma yin biyayya gare su, sannan ya bukaci al’ummar Musulmi da su hada kai a matsayin ’yan uwan juna.
“Dole ne mu tuna da muhimmancin shugabanci, hadin kai da kyautata zaman tare tsakanin Musulmi da kuma tsakaninsu da Kiristoci a irin halin da kasar nan ke ciki,” in ji shi.
A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Malamai ta JIBWIS, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya shawarci alkalai da su guji cin hanci, sannan masu rike da mukaman gwamnati su kasance masu tsare gaskiya da rikon amana wajen tafiyar da harkokin ofishinsu.