✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsadar rayuwa: Bankin Afirka ya tallafawa Najeriya da dala miliyan 540

Bankin Raya Kasashen Afirka (AfDB) ya fara raba tallafin kudi Dalar Amurka Miliyan 540 ga wasu jihohi takwas a Najeriya

Bankin Raya Kasashen Afirka (AfDB) ya fara raba tallafin kudi Dalar Amurka Miliyan 540 ga wasu jihohi takwas a Najeriya.

Tallafin na daga cikin yunkurin bankin AfDB na samar da isasshen Abinci ga jama’a tare da sarrafa shi, yayin da ’yan kasar ke kokawa kan tsadar rayuwa.

Masana dai na ganin cewa rashin fitar da kayayyaki zuwa kasuwar duniya, da kuma dogaro da kayan kasashen waje ne abin da ya jefa kasar cikin halin tsadar rayuwa da ake fuskanta a halin yanzu.

Haka zalika, kuma hauhawar farashin kayaya jefa kananan yan kasuwa cikin  zulumi sakamakon karyewar darajar kudin kasar, inda dalar Amurka ke ci gaba da ccin karenta babu babbaka.

’Yan Najeriya dai na ganin gazawar gwamnatin kasar wajen dogaro da man fetur, alhalin kasar tana da arzikin ma’adanai da na noma.