✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsadar kayan masarufi a mahangar Musulunci (1)

Daga Hudubar Sheikh Ibrahim bn Saleh Al-Ajlan,Masallacin Sheik bn Baz, Riyad, Saudiyya Huduba ta farko Godiya da taslimi:Bayan haka, halin da muke ciki ya komai…

Daga Hudubar Sheikh Ibrahim bn Saleh Al-Ajlan,
Masallacin Sheik bn Baz, Riyad, Saudiyya
Huduba ta farko

Godiya da taslimi:
Bayan haka, halin da muke ciki ya komai ya kwabe, rayuwa ta gumama, babba da yaro na dandanawa, mai kudi da fakiri na jin jiki har ya zamo hakan ne abin  da aka fi tattaunawa a ko’ina a tsakanin masu hankali da sauran jama’a, kuma jaridu da kafafen watsa labarai ke ruwaitowa kuma kullum ke ci gaba da hauhawa.
Hali ne da yake dada jefa fakirai cikin wahala, kuma masu matsakaicin samu suke karyewa. Hali ne da masu hankalin cikin al’umma suka gaza magance shi, ya zamo kamar wata cuta da ta shige musu duhu, ya zamo ya fi wasu matsaloli da aka saba gani kamar sata da son kai da makamantansu. Wannan hali shi ne matsalar tsadar kayan masarufi ko kayan abinci.
Ya ’yan uwa a cikin imani! Hakika kasarmu da sauran kasashen Musulmi suna fuskantar tsadar kayan masarufi da tsadar rayuwa, kuma wannan tsada ta shafi kusan komai na rayuwa na daga abinci da gidajen zama da ababen hawa da sutura da magunguna da jinya, har ta tatuke ajifan mutane da dama ta yadda wadansu ba su iya fuskantar wannan kuncin rayuwa sai sun hada da bashi. Amma ga talakawa da dama suke rayuwar hannu-baka-hannun-kwarya wannan tsada ta kara musu kunci ne a kan kuncinsu!
To amma – ya ku bayin Allah- ya wajaba mu duba mu ga abin da ke kawo wannan tsada da kuncin rayuwa da kuma yadda za mu fuskanci haka.
Fuska ta farko:
Wannan tsada babu shakka tana da dalilai na fili a fannin tattalin arziki da suka hada da sauye-sauye ko faduwar darajar man fetur da karayar tattaln arziki da muke fuskanta da sauransu.
Sai dai ga mu Musulmi, bai kamata mu tsaya kan wannan ma’ana ta abin duniya, ba tare da mun dubi dalilai na boye na shari’a ba, wadanda su ne galibin abin da Littafin Ubangijinmu da Sunnar Annabinmu (SAW) suke nusar da mu a kai.
Ya bayin Allah! Hakika ayoyin Mai rahama da Hadisan Shugaban ’ya’yan Adam (SAW) da dama sun nuna cewa abin da yake samun bayi na kunci da bala’i da masifu da wahala, sababinsu shi ne irin abin da mutane suke aikatawa na zunubi da sabo.
Wannan manufa wajibi ne ta zauna a cikin zukatanmu, mu rika sanya ta a gaba a duk lokacin da muke son magana a kan wannan mushkila. Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma abin da ya same ku na wata masifa, to game da abin da hannayenku suka sana’anta ne, kuma Allah Yana yafewar (wadansu) laifuffuka) masu yawa.” (k:42:30). Allah Ya yi gaskiya kuma wane ne ya fi Allah gaskiyar zance? Ya kara da cewa: “Shin kuma a lokacin da wata masifa hakika ta same ku alhali kun samar da biyunta, kun ce: “Daga ina wannan yake?” Ka ce: “Daga wurin rayukanku yake.” (k:3:165).
Wata rana Annabi (SAW) ya je ga sahabbansa ya ce: “Ya ku taron Muhajirai! Abubuwa biyar idan aka jarrabe ku da su, -kuma ina neman tsarin Allah a ce kun riske su-. Wato alfasha ba za ta bayyana a cikin wata al’umma ba, face an yawaita musu ambaliya da yunwa a cikinsu irin wadanda ba su kasance a cikin magabatansu ba. Kuma ba za su nakasa mudu da sikeli ba, face an kama su shekaru (fari) da tsadar kayan abinci da zaluncin mai mulki a kansu. Kuma ba za su hana zakkar dukiyarsu ba, face an hana su koda digon ruwa daga masa ba. Ba domin dabbobinsu ba ba za a yi musu ruwa ba. Kuma ba za su warware alkawarin Allah da ManzonSa (SAW) ba, face Allah Ya dora makiyinsu daga wajensu ya rika kwace abin da suka mallaka. Kuma shugabanninsu ba za su bar hukunci da Littafin Allah ba, su ki abin da Allah Ya zaba ba, face Allah Ya sanya bala’insu a tsakaninsu.” (Ibn Majah da Baihaki suka ruwaito shi, kuma Alhakim ya inganta shi, kuma shi Hadisi ne Hasnun).
Magabatan kwarai na wannan al’umma sun kasance idan aka saukar da kunci da wahala aka samu bala’o’i, sukan ce ba a saukar da bala’i sai ana aikata zunubi kuma ba za a dauke shi ba, sai an koma ga Allah an tuba.
Wani magabacin kwarai ya ce sakamakon aikin sabo shi ne: “Rauni a cikin ibada da kunci a cikin rayuwa.”
Yana daga cikin sunnonin Allah Ya saka wa mutane da jinsin aikinsu, idan al’umma ta munana ni’imar dukiya ta saba wa Allah da ita, sai Allah Ya sanya ukubarsu a cikin wannan dukiya, kuma daga cikin ukubobin akwai tsadar kayan masarufi.  Don haka wajibi ne a kan al’umma idan ta hadu da tashin farashin kayan abinci da na masarufi ta tuba zuwa ga Ubangijinta, ta nemi gafarar kura-kuranta na cikin al’amuran dukiya, wadda jagabansu ita ce riba da cin hanci da rashawa wadanda Allah Ya la’anci ma’abutansu, sai kuma caca.  Sannan akwai wasu da suka hada da algushu da karya a cikin saye da sayarwa da sauran abubuwan da suka saba wa shari’a a harkokin neman dukiya.
Fuska ta biyu:
Lallai wannan tsada wani nau’i da sakayya ne daga masifun da Allah Ya kaddara su a kan wannan al’umma a matsayin daya daga cikin masifun da za a rika jarrabar wannan al’umma da su. Hakika Al-Mustapha (SAW) ya bayar da labarin cewa: “Lallai wannan al’umma an sanya karshenta a cikin farkonta, kuma da sannun bala’i da al’amuran da kuke ki za su samu karshenta.” Muslim ya ruwaito.
Don haka babu shakka -ya ku bayin Allah!- cewa lallai tsadar kayan abinci da duk wani bala’i da muke haduwa da shi jarrabawa ce ga imanin bayi, ana auna irin bautarsu ne ga Allah a cikin tsanani. Kuma wannan sunna ce ta Mahalicci ga al’ummomin da suka gabata. Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma lallai Mun aika zuwa ga al’ummomi daga gabaninka, sai Muka kama su da tsanani da cuta, tsammaninsu za su yi kankan da kai.” (k:6:42). Kuma Ya fadi game da Bani Isra’ila: “…Muka jarrabe su da abubuwan alheri da na masifa: tsammaninsu suna komowa (ga Allah)” (k:7:168).
A irin wadannan halaye ne imanin masu gaskiya ke bayyana, wanda kuma yake bauta wa Allah a karkace ya fadi. Idan bawa ya bayyana shukura ga Ubangijinsa ta wajen sadakokinsa tare da yaye wa mabukata bakin cikinsu, sai ya kai kansa ga matsayin masu yawan kyauta, sai ya tsira ya kuma samu babban rabo. Amma idan ya rika kuka ya nuna gazawa ya fusatar ya ci gaba da tara dukiyar haram, hakika ya tabe ya yi asara. Kuma Allah Ya yi gaskiya cikin fadinSa: “Allah bai kasance yana barin muminai a kan abin da kuke kansa ba, sai Ya rarrabe mummuna daga mai kyau.” (k:3:179).   
Fuska ta uku:
Ya bayin Allah! Mafi yawan mutanen da suka fi cutuwa da shan wahalar wannan tsada su ne talakawa da miskinai, wahalhalunsu sun dada yawa bakin cikinsu ya yawaita, suna fama da tsadar da rashin abin saye. Wannan shi ne halinsu kamar yadda wani mawaki ya rera:
“Fakiri a lokacin yunwa ba ya barci,
Miskini kuma yana fama da bakin ciki.
Marar abin rayuwa a takure,
A wurin iyalinsa abin zargi ne.
Yana can yana nema wasu mutane na barci,
A kan dimbin dukiya suke zaune.”
Yana daga cikin alamar kyautatuwar al’umma da tabbatar alheri a cikinta a samu tausaya wa wadannan jinsin mutane, tare da misalta wasiyyar Annabi (SAW) game da su inda ya ce: “Ku neme ni ta wurin masu rauni, abin sani ana azurta ku ana taimakonku ne saboda raunana. Ma’ana albarkar addu’arsu da salihancinsu).”
Fuska ta hudu:
Yak u ’yan kasuwa da attajirai! Ya ku ’yan kasuwa da attajirai! Da wannan kira Al-Mustapha (SAW) ya daga muryarsa, sai mutane suka juyo gare shi, idanuwa suka koma kansa sannan ya ce: “Lallai ’yan kasuwa, wallahi za a tashe su suna fajirai a Ranar kiyama sai wanda ya yi takawa ya yi da’a kuma ya yi sadaka.” Tirmizi ya ruwaito shi kuma Hadisi ne ingantacce.
Don haka ya kai wanda Allah Ya bai wa dukiya! Ka yi tunani cew lallai ne rahamar Allah tana jiranka idan ka yi mu’amala da bayin Allah cikin sassauci da kyautatawa.  A cikin wani Hadisi Annabi (SAW) ya ce: “Allah Ya yi rahama ga mutumin da yake sassauci da tausayawa idan zai sayar ko idan zai saya ko idan zai yi hukunci.” Buhari ya ruwaito shi a cikin sahihinsa.
Wallahi duk wanda yake jawo tsadar kaya bai san kyautatawa ba bai san sauki ba, domin jawo tsadar kaya da yake yi tana jawo kunci ga waninsa, kamar yana dada tura mutane ne cikin kunci da fatar su dada shiga damuwa. A cikin wani Hadisi da Muslim ya ruwaito Annabi (SAW) ya ce: “Wanda ya karbi dukiya da hakkinsa Allah zai sanya albarka a cikinta, amma wanda ya karbi dukiya ba tare da hakki ba, to misalinsa kamar misalign wanda yake cin abinci ne amma ba ya koshi.”
Don haka dan uwa dan kasuwa Musulmi ka tuna cewa, lallai yin rahusar kayayyaki ga Musulmi da kawar musu da tsanani da rashin tsauwala musu kudin kayayyaki alamu ne na rahama a zuciyar mai yin haka da kuma tsarkin zuciyarsa kuma irin wadannan su ne wadanda ake yi musu alkwarin karuwar albarka a cikin arzikinsu da yalwatuwar dukiyarsu da samun dacewa a rayuwarsu in Allah Ya so.