✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsadar hatsi na neman fin karfin mutane a Kaduna

Ana zargin ’yan kasuwa na boye hatsi domin neman kazamar riba

Mazauna Jihar Kaduna na kokawa kan ci gaba da tashin farasin hatsi musamman masara, wake da gero a kasuwanni.

Mutanen na zargin hakan na da nasaba da ayyukan ’yan kasuwa masu taskace hatsi domin neman kazamar riba.

A Kasuwar Tudun Saibu, daya daga cikin manya kasuwannin hatsi na mako-mako a Karamar Hukumar Sabon Gari, Aminiya ta gano cewa farashin hatsi ya yi tashin gwauron zabo.

A zagayen da wakilinmu ya yi, ya gano cewa tun farkon shekarar 2021 da muke ciki kayan abincin suka yi wannan tsadar da ke neman fin karfin talaka.

Sarkin Kasuwar Tudun Saibu, Alhaji Usman Danasabe, ya shaida wa wakilinmu cewa farashin babban buhun shinkafa da aka saryar N14,000 a ranar 31 ga Disambar, 2020 ya tashi zuwa N17,000 a halin yanzu.

Buhun waken soya da a aka rika sayarwa N22,000 da na farin wake da ake sayarwa N23,000 yanzu duk sun koma N30,000.

Ya kara da cewa buhun gero da aka sayar N18,000 a wancan lokacin kuma ya tashi zuwa N20,000.

’Yan kasuwa na boye hatsi

Alhaji Usman ya ce ’yan kasuwa na boye kayan abincin kuma duk sati ’yan kasuwa na yin turuwar sayen hatsi a kasuwar daga Jihohin Kano, Legas, Abuja da Kaduna da Jamhuriyar Nijar da sauran wurare.

Wasu mutanen da Aminiya ta zanta da su sun ce tsadar hatsin na neman fin karfin aljihunsu, don haka suka yi kira ga gwamnati da ta fara kayyade farashinsa.

Wani jami’in tsaro a Kaduna, Adamu Ibrahim, ya ce ba zai iya sayen wake ba yanzu saboda farashin karamin kwanon waken ya koma N500.

Ya ce yawancin ’yan kasuwar na zargin kananan dillalai da kuma dokar hana fitar da aka sanya na COVID-19 a matsayin ummulhaba’isin farashin kayan.

Suna kuma bayyana saurin daukewar ruwan sama da aka samu a matsayin dalilin samun karancin amfanin gona da ake girbe.

Danasabe ya yi kira ga gwamnati da ta taimaka wa masu noman rani da kayan aiki domin rage tsadar hatsi da kuma samar da wadataccen abinci a cikin kasa.

Farashin kayan gwarri ya sauka

Sai dai kuma a daya bangaren, Alhaji Garba Alhassan, ya ce farashin kayan gwari ya fadi warwas a kasuwanni.

Ya ce yanzu haka ana sayar da babban kwandon tumatir a kan N2,000.

A cewarsa, babban buhun tattasai kuma yanzu ana sayar da shi ne N4,000, sai albasa da farashin buhunsa ya koma N15,000.